Zamfara: Ƴan Bindiga Sun Harbe Shugaban PDP, an Sace Ɗan Siyasa da Wasu Mutum 2
- ’Yan bindiga sun kai hari a hanyar Manyaci zuwa Bukkuyum, inda suka bude wuta kan wata mota dauke da shugaban PDP na karamar hukuma
- An harbi Hon. Muhammad Sala Wuta a hannu da kafa yayin da yake kan hanyar zuwa Bukkuyum tare da wasu ’yan jam’iyya a cikin mota
- An sace mutane uku ciki har da Hon. Mu’azu Zannan Gwashi a yayin harin, lamarin da ya girgiza al’ummar Bukkuyum da kewaye
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Hare-haren yan bindiga na kara kamari musamman a yankunan Arewa maso Yammacin Najeriya.
Mahara suna cin karensu babu babbaka musamman a ƙauyukan yankin wanda yan siyasa ma ba su tsira ba.

Source: Twitter
Zamfara: 'Yan bindiga sun budewa yan siyasa wuta
Rahoton Bakatsine ya tabbatar a shafinsa na X cewa an kai wa shugaban PDP hari da mukarrabansa.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa yan bindiga sun budewa motar shugaban jam'iyyar na karamar hukumar Bukkuyum wuta.
Lamarin ya faru ne a jiya Talata 22 ga watan Yulin 2025 yayin da suka samu munanan raunuka.
Harin yan bindiga: Halin da shugaban PDP ke ciki
An harbi Hon. Muhammad Sala a kan hanyarsa ta zuwa Bukkuyum tare da Hon. Mu'azu Muhammad Gwashi.
An ce Hon. Sala ya samu raunuka dalilin harbin bindiga a hannu da kafa yayin da aka sace wasu mutum uku.
Daga cikin wadanda aka sacen akwai Hon. Mu’azu Zannan Gwashi da wasu da suke tare da shi yayin harin wanda ya firgita al'ummar yankin.
Sanarwar ta ce:
"A Yammacin jiya, ’yan bindiga sun tare hanya tsakanin Manyaci da Bukkuyum inda suka bude wuta kan wata mota.
"Shugaban jam’iyyar PDP a karamar hukumar Bukkuyum, Hon. Muhammad Sala Wuta, ya samu harbin bindiga a hannu da kafa.
"An sace mutane uku ciki har da Hon. Mu’azu Zannan Gwashi."

Source: Original
An garzaya da Hon. Sala asibiti a Zamfara
Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa an garzaya da Hon. Sala asibiti da raunuka a jikinsa domin ba shi kulawar gaggawa.
Wasu mutanen yankin sun bukaci hukumomi da su yi kokarin kawo karshen hare-haren yan bindiga da suka addabi garuruwa da dama wanda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi.
Al'umma da dama sun yi ta yi wa shugaban fatan alheri da samun sauki bayan tsautsayin da ya faru da su a hanyar Bukkuyum da ke jihar Zamfara.
'Yan bindiga sun farmaki matafiya a Zamfara
Mun ba ku labarin cewa yan bindiga ɗauke da makamai sun yi ta'asa kan matafiya a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
Miyagun ƴan bindigan sun hallaka fasinjoji bakwai bayan sun buɗe wa motarsu wuta lokacin da suke tafiya ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.
Rahotanni sun bayyana cewa ƴan bindigan sun zo tsallaka titi ne lokacin da suka buɗe wuta ga motar wacce ke tafiya da fasinjoji a kan hanyar Gusau-Funtua domin harkokin kasuwanci da lamuransu da yau da kullum.
Asali: Legit.ng

