Fulani Makiyaya Sun Dimauce da aka kai Musu Hari da Dare, an Sace Shanu

Fulani Makiyaya Sun Dimauce da aka kai Musu Hari da Dare, an Sace Shanu

  • Wasu 'yan fashi dauke da makamai sun kai farmaki kauyen Dutsen Wai da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna
  • Wani rahoto ya bayyana cewa maharan sun yi harbi sama don tsorata jama'a, sannan suka kwashe dabbobi da dama
  • Rundunar 'yan sanda da sojoji sun fara bincike tare da hadin gwiwar masu sa-kai domin gano inda 'yan fashin suka nufa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - An kai hari kan makiyaya a kauyen Dutsen Wai da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin dimuwa da kunci.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu 'yan fashi dauke da manyan makamai sun kai farmaki da misalin karfe 10:00 na dare a ranar Litinin.

An sace shanun Fulani a jihar Kaduna
An sace shanun Fulani a jihar Kaduna. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Mai sharhi kan lamuran tsaro, Zagazola Makama ne ya wallafa labarin kai harin a shafinsa na X a yau Laraba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun nuna tsaurin ido, sun sace mutane 26 a mahaifar gwamnan Bauchi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan lamari ya kara tabbatar da yadda matsalar satar shanu ke ci gaba da addabar yankunan Arewa maso Yammacin Najeriya.

An kai wa Fulani hari da dare a Kaduna

Wani mazaunin yankin mai suna Yusuf Abdullahi ya bayyana cewa 'yan fashin sun shigo kauyen ba zato ba tsammani.

A cewarsa, sun yi harbi sama don tsorata makiyaya, sannan suka jefa shanun cikin daji, suna harbin duk wanda ya kusanto su.

An sace shanun manyan makiyaya a Kaduna

Rahotanni sun ce dabbobin da aka sace na wasu fitattun makiyaya ne a yankin, ciki har da Alhaji Ibrahim Abubakar, Alhaji Musa Abubakar da Usman Isiya.

Wani dan uwan ga daya daga cikin wadanda abin ya shafa ya ce:

"Wannan hari ne don kawar da rayuwarmu gaba daya."

Sojoji sun shiga daji domin neman shanun

Sojojin Operation Fansan Yamma tare da jami’an tsaro sun samu kiran gaggawa da misalin karfe 6:00 na safiyar Talata.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi bayani yayin da aka fara taron daidaita farashin fetur a Abuja

Bayan hakan, sun fantsama cikin daji da ke kewaye da wajen domin bincike da kokarin kama 'yan fashin da kuma gano inda aka boye dabbobin.

Gwamnan jihar Kaduna yayin wani taro
Gwamnan jihar Kaduna yayin wani taro. Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

'Yan sanda sun dauki mataki bayan satar shanun

Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da cewa suna yin aiki tukuru domin gano wadanda suka aikata laifin.

Wani babban jami'in 'yan sanda da ya nemi a boye sunansa ya ce:

"Mun tura tawagar sintiri cikin daji kuma muna aiki tare da masu sa-kai."

Matsalar satar shanu ta dade tana addabar Arewa maso yammacin Najeriya, tana kuma haddasa barazanar tsaro da kuma tashe-tashen hankula.

Bayan asarar dukiya, wannan matsalar tana haddasa rikici, hijira da kuma tabarbarewar zamantakewa a yankunan da abin ke faruwa.

Amurka ta yi magana kan 'yan bindiga

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Amurka ta ce matsalar tsaro na kara ta'azzara a Najeriya da wasu kasashen Afrika.

Gwamnatin ta bayyana wasu jihohin Najeriya da ta ce ana fama da matsalar masu garkuwa da mutane, fashi da sauransu.

Ta gargadi 'yan kasarta da su kaucewa ziyartar jihohin da ta ayyana tare da yin tanadi na musamman a kan harkar lafiya yayin zuwa Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng