Shugaba Tinubu Ya Manta da Siyasa, Ya Ba 'Yan Najeriya Sabon Tabbaci
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa na ƙoƙari wajen yaƙi da ta'addanci
- Mai girma Bola Tinubu ya bayyana cewa yaƙi da ta'addanci na daga cikin abubuwan da gwamnatinsa ta fi mayar da hankali a kai
- Ya ba mutanen da matsalar tsaro ta shafa, tabbacin cewa yana sane da su kuma zai share musu hawaye
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba ƴan Najeriya tabbaci kan abubuwan da gwamnatinsa ta sanya a gaba.
Shugaba Tinubu ya tabbatar wa ƴan Najeriya cewa yaƙi da ta’addanci da ayyukan ƴan bindiga na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta fi bai wa fifiko.

Source: Facebook
Tashar Channels tv ta ce Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne lokacin ƙaddamar da zagayen farko na gidajen da aka ginawa mutanen da hare-haren ƴan bindiga suka shafa a Kaduna a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya ƙaddamar da gidaje a Kaduna
Shugaba Tinubu ya samu wakilcin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu.
Aikin gina gidajen, wanda aka aiwatar tare da haɗin gwiwar gidauniyar Qatar Charity Organisation, na daga cikin shirin gwamnatin tarayya na sake gina ƙauyukan da suka tarwatse sakamakon hare-haren ƴan bindiga.
“Yaƙi da ta’addanci babban ƙalubale ne, amma magance shi na daga cikin manyan abubuwan da wannan gwamnati ke mayar da hankali akai a ƙarƙashin ajandar tsaron ƙasa."
"Najeriya na hannu nagari, kuma za mu dawo da doka da oda. Wannan tabbaci ne da muke bayarwa. Za a cimma hakan, in sha Allah."
- Shugaba Bola Tinubu
Shugaban ƙasan ya bayyana cewa an samu gagarumar nasara a ƙoƙarin dawo da zaman lafiya da sake farfaɗo da rayuwar jama’a a jihar Kaduna, rahoton The Punch ya tabbatar.
Ya jaddada cewa kyakkyawan shugabanci na buƙatar fifita buƙatun jama’a, musamman waɗanda rikici ya shafa.

Kara karanta wannan
"An kusa fara ganin saƙon kudi," Gwamnatin Tinubu za ta fara biyan ƴan N Power kuɗinsu
"Ana ci gaba da farfaɗowa, kuma a bayyane yake cewa sabon yanayi ya zo a jihar Kaduna, abubuwa na canzawa."
"Muna share hawayen waɗanda rikici ya shafa. Muna sulhunta al’umma. Muna bai wa kowa dama da jin cewa ya na da muhimmanci."
- Shugaba Bola Tinubu
Tinubu ya kwararo yabo ga hafsoshin tsaro
Shugaban ƙasan ya yabawa gwamnatin jihar Kaduna, ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro, da kuma Babban Hafsan Tsaro na ƙasa saboda matakan da suka ɗauka, ta hanyar amfani da dabarun soji da kuma hanyoyin sulhu don shawo kan matsalolin tsaro a yankin.

Source: Facebook
A cewarsa, buɗe kasuwar Birnin Gwari da dawowar manoma zuwa gonakinsu alamu ne na ci gaba.
"Wannan a bayyana ake nunawa jama'a cewa Kaduna ta samu sabon yanayi, wanda yake na gaskiya da ci gaba."
- Shugaba Bola Tinubu
Yayin da yake jawabi ga waɗanda suka tsira daga hare-haren, shugaban ƙasan ya ƙara da cewa:
"Mun ji kukanku. Kun fuskanci tashin hankali matuƙa, amma muna tare da ku. Gwamnatinku na kallon ku, kuma tana jin raɗaɗin ku."

Kara karanta wannan
'Za mu iya aiki tare,' Abin da Kwankwaso ya fada bayan haduwa da Tinubu a Aso Villa
Gwamna ya yi hasashen nasarar Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya nuna goyon bayansa ga tazarcen Shugaba Bola Tinubu.
Gwamna Nwifuru ya bayyana cewa Tinubu zai lashe zaɓen 2027 duk kuwa da taruwar ƴan adawa a waje ɗaya ƙarƙashin haɗaka.
Ya bayyana cewa ƴan siyasar da ke ƙarƙashin haɗaka ba su isa su hana tazarcen Tinubu ba a 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
