'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Yi Awon Gaba da Jami'in Gwamnati a Borno
- Ƴan ta'adda da ake zargin mayaƙan ƙungiyar Boko Haram ne sun yi aika-aika a jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya
- Miyagun sun tare wata mota inda suka yi awon gaba da wani jami'in gwamnati lokacin da yake tsaka da tafiya tare da wasu mutane
- Bayan sace jami'in gwamnatin dai, an tura jami'an tsaro domin bin sawun ƴan ta'addan da yiwuwar ceto shi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Wasu ƴan ta'adda da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun sace jami'in gwamnati da wani mutum a jihar Borno.
Ƴan ta'addan na Boko Haram sun sace sakataren ƙaramar hukumar Kukawa ta jihar Borno tare da wani mutum guda.

Source: Facebook
Majiyoyi daga mazauna yankin da na tsaro sun tabbatar wa da jaridar Daily Trust faruwar lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan Boko Haram sun sace jami'in gwamnati
An tattaro cewa sace mutanen ta faru ne da misalin ƙarfe 1:35 na rana a ranar Talata a Garin Kashim, yayin da waɗanda aka sace suke tafiya zuwa Kukawa a cikin wata mota ƙirar Volkswagen Golf.
"Mayaƙan sun tare motar, suka umurci sakataren da ɗaya daga cikin fasinjojin da su sauka, sannan suka bar sauran fasinjojin su ci gaba da tafiya.
“Bayan haka sai suka tafi da sabon sakataren da ya fara aiki a ƙaramar hukumar da sauran mutum ɗayan da suka sace zuwa cikin daji."
- Wata majiya daga ɓangaren tsaro
Ana zargin akwai hannun masu ba da bayanai
Wani mazaunin yankin ya danganta faruwar lamarin da yiwuwar samun bayanai daga masu kai rahoto ga ƴan ta'adda a yankin da sakataren ya fito.
"Ƴan ta'addan sun ɓoye kusa da kogi suka jira motar Golf ta iso. Kai tsaye suka nufi sakataren da ɗayan mutumin. Wannan aikin masu kai bayani ne."
- Wata majiya
Ya ƙara da cewa rundunar sojoji ta Sector 3 ta baza jami’an tsaro domin tunkarar lamarin.
“Mun yi kiran gaggawa zuwa Sector 3, kuma nan take suka tura sojoji domin bin sahu da ƙoƙarin ceto waɗanda aka sace."
- Wata majiya

Source: Original
Ƙaramar hukumar Kukawa na cikin yankin tafkin Chadi, inda mayaƙan Boko Haram ke addabar mazauna yankin da matafiya.
Lamarin ya faru ne kwanaki biyu bayan wasu mayaƙan kungiyar ISWAP sun kashe mutane bakwai ciki har mafarauta, ƴan ƙungiyar CJTF da masu tsaron al’umma a ƙaramar hukumar Magumeri ta jihar Borno.
Sojoji sun hallaka ƴan ta'addan Boko Haram
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun yi raga-raga da ƴan ta'addan Boko Haram a wasu hare-hare da suka kai musu.
Sojojin sun hallaka ƴan ta'adda 24 bayan sun kai hare-hare ta sama da ƙasa a maɓoyarsu da ke jihohin Borno da Adamawa.
Jami'an tsaron sun kuma samu nasarar ƙwato makamai masu tarin yawa a hannun miyagun ƴan ta'addan tare da raunata da dama daga cikinsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

