Bayan Shekaru 2, Minista Ya Fito Fili Ya Faɗi abin da Ya Hana Tinubu Naɗa Jakadu

Bayan Shekaru 2, Minista Ya Fito Fili Ya Faɗi abin da Ya Hana Tinubu Naɗa Jakadu

  • Jam’iyyar ADC ta soki gwamnatin Bola Tinubu kan jinkirin nadin jakadu, tana cewa hakan yana rage martabar Najeriya a ƙasashen waje
  • Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta mayar da martani, inda ta ce Tinubu ya jinkirta nadin jakadu domin gyara tsarin nadin wakilan
  • Gwamnatin tarayya ta ce Najeriya tana da wakilci a ofisoshin diflomasiyyar ta na duniya, kuma ta gargadi ADC kan rage wa ƙasar ƙima

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta yi martani ga sukar da jam’iyyar ADC ta yi kan jinkirin nadin jakadu da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yi.

A cikin wata sanarwa da Bolaji Abdullahi, mai magana da yawun rikon ADC ya fitar a ranar Lahadi, ya zargi Tinubu da jinkirta nadin jakadun.

Ministan harkokin waje ya yi magana kan nasdin jakadu bayan shekaru 2
Ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar ya kare jinkirin Tinubu na nadin jakadu. Hoto: @NigeriaMFA
Source: Twitter

ADC ta caccaki Tinubu kan nada jakadu

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi bayani yayin da aka fara taron daidaita farashin fetur a Abuja

A sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X, Bolaji ya bayyana cewa jinkirta nadin jakadun ya rage ingancin hulɗar Najeriya da ƙasashen da ake da ofisoshin jakadanci a cikinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce sababbin matakan da su Amurka da UAE suka ɗauka kan tsarin bizar Najeriya, hujja ce da ke nuna gazawar jakadanci, saboda rashin kasancewar jakadu a kasashen.

Sanarwarsa ta ce:

"ADC ta lura cewa kin amincewar gwamnatin Tinubu na naɗa jakadu bayan shekaru biyu a kan mulki yana nuna yadda take da makarkashiya ga ƙasar da kuma cikakken rashin fahimtar abin da ake buƙata don mulkin muhimmiyar ƙasa kamar Najeriya."

Gwamnati ta yi martani ga jam'iyyar ADC

Amma a ranar Talata, Alkasim Abdulkadir, mai magana da yawun ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, ya yi martani kan kalaman ADC, inji rahoton The Cable.

Alkasim Abdulkadir, ya bayyana wannan suka ta ADC a matsayin “marar tushe” kuma “wacce aka yi ta a kan siyasa kawai”.

Ya ce jinkirin nadin jakadu ya samo asali ne daga gyaran da Shugaba Tinubu ke yi wa tsarin harkokin waje na Najeriya, domin tabbatar da cewa nadin jakadu na gaba zai ta’allaka ne da cancanta, ƙwarewa da gaskiya, ba wai don ra'ayin siyasa kawai ba.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An gano abin da ya hana Atiku shiga ADC bayan ya baro Jam'iyyar PDP

“Nadin jakadu ba wani abu ba ne da za a yi bisa ra’ayi ko don biyan bukatar wasu jam’iyyun siyasa ba.
"Wannan aiki ne na kasa wanda ya kamata a yi shi cikin tsari, bisa la’akari da bukatun tsaron kasa da matsayin Najeriya a duniya."

- Alkasim Abdulkadir.

Ministan harkokin waje ya ce Tinubu zai yi amfani da cancanta wajen nada jakadu
Ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar. Hoto: @NigeriaMFA
Source: Twitter

"Har yanzu Najeriya na da jakadanci" - Alkasim

Ya kara da cewa an daina nadin jakadu a matsayin sakayya ga ’yan siyasa ba tare da ƙwarewar diflomasiyya ba, domin hakan ya saba wa tsarin duniya na yanzu.

Alkasim ya kuma bayyana cewa har yanzu Najeriya tana da wakilci a dukkan ofisoshin ta na waje ta hannun chargé d’affaires (manyan wakilan kasa kafin a nada jakadu).

Ya kuma ya bukaci jam’iyyar ADC da kada ta rage wa Najeriya ƙima ta hanyar zargin diflomasiyyar ƙasar da rashin inganci.

"Matsalar kudi ta hana nadin jakadu" - Tuggar

Tun da fari, mun ruwaito cewa, an bayyana matsin tattali da karancin kudi a matsayin dalilan da suka hana Shugaba Bola Tinubu bai nada jakadu a ƙasashen.

Kara karanta wannan

"Ina wutar da ka yi alkawari?": ADC ta jefawa Tinubu tambaya da ya kamata ya amsa

Ministan harkokin waje, Ambasada Yusuf Tuggar, ya ce Najeriya na fama da matsalolin kuɗi da rikicin tattalin arziki da suka shafi yanke shawarar nadin manyan jami’an diflomasiyya.

A halin yanzu, Najeriya na da ofisoshin diflomasiyya guda 109, ciki har da ofisoshin jakadanci 76, manyan hukumomi 22 da kuma ofisoshi ƙanana 11 a sassa daban-daban na duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com