ICRC Ta Gano Babbar Matsalar da Ta Tunkaro Arewa sakamakon Ta'addanci

ICRC Ta Gano Babbar Matsalar da Ta Tunkaro Arewa sakamakon Ta'addanci

  • Fiye da mutane miliyan 3.7 a Arewa maso Gabas na fama da yunwa mai tsanani, sakamakon rikici da tashe-tashen hankula da ya yi 'kamari
  • 'Kungiyar bayar da agaji ta 'kasa da 'kasa (ICRC) ce ta bayyana hakan, inda ta ce matsalar na 'kara gaba, kuma ta fi shafar yara 'kanana
  • Sai dai 'kungiyar ta bayyana shirinta na tallafa wa manoman domin a farfado da lafiya yara 'yan kasa da shekaru biyar da mata masu juna biyu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Hukumar Agaji ta Ƙasa da Ƙasa ta ICRC, ta bayyana damuwa kan tsanantar yunwa da matsin tattalin arziki a yankunan da rikici ya shafa a Arewa maso Gabashin Najeriya.

ICRC ta ce fiye da mutane miliyan 3.7 na fama da rashin isasshen abinci a wannan yanki baya ga rashin tsaro da ya hana su zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun tare Sanata Natasha, sun hana ta shiga ofis a Majalisa

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da abinci
ICRC ta ce akwai yunwa a Arewa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed/Getty
Source: Facebook

Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa Aliyu Dawobe, jami’in hulɗa da jama’a na ICRC a Najeriya, ne ya fitar da sanarwar a ranar Litinin a birnin Abuja.

Yunwa ta sako 'yan Arewa a gaba

Jaridar Vanguard News ta bayyana cewa Dawobe ya ce yawancin mutanen da abin ya shafa a baya manoma ne da ke ciyar da al’ummominsu.

Sanarwar ta nuna cewa tashe-tashen hankula da rikice-rikice sun tilasta wa iyalai barin gidajensu, sun hana su komawa gona, tare da tarwatsa tsarin samar da abinci a yankunan.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
ICRC ta ce yunwa na ragargaza yara da mata Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ita ma Shugabar ofishin ICRC a Maiduguri, Diana Japaridze, ta bayyana cewa jama'a na kara tsunduma a cikin matsala yayin da abinci ke kara karanci.

A cewarta:

“Wannan lokaci ne da iyalai ke bukatar fara siyan abinci, amma da dama daga cikin wadanda rikici ya shafa ba za su iya siyan shi ba.”

Matsalar abinci na kamari a Arewa

Ta kara da cewa matsalar rashin abinci na haifar da karancin gina jiki, musamman ga yara ’yan kasa da shekaru biyar, da kuma mata masu juna biyu da masu shayarwa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Mamakon ruwan sama ya jawo ambaliya a gari, mutane 54 sun mutu

A cewarta:

“ICRC tana tallafa wa cibiyoyin kula da matsalar rashin abinci mai gina jiki, tare da shirya fadakarwa a cikin al’umma domin taimaka wa iyalai wajen kula da yara masu rauni.”

Japaridze ta ƙara da cewa domin magance tushen matsalar yunwa da kuma karfafa wa jama'a, ICRC ta ƙaddamar da shirin tallafa wa harkar noma a yankin.

“Shirin yana tallafa wa noman damina da noman rani, kuma an shirya shi ne don taimaka wa dubunnan iyalai da ke noma.”

Tinubu: 'Akwai yunwa a 'kasa'

A wani labarin, mun wallafa cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin Bola Ahmed Tinubu ta dauki matakin gaggawa bayan amincewa da cewa Najeriya na fama da yunwa mai tsanani.

Wannan na zuwa bayan mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya kaddamar da kwamitin yaƙi da yunwa a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a ranar Juma’a, 12 ga Yuli 2025.

Ya ƙara da bayyana cewa gwamnatin tarayya ta shiga tattaunawa da gwamnonin jihohi da masana a fannin abinci da noma domin nemo mafita mai ɗorewa kan matsalar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng