An Zargi Gwamnati da Hannu a Watsar da Aikin Titin Kano zuwa Katsina, Ana Asarar Rayuka

An Zargi Gwamnati da Hannu a Watsar da Aikin Titin Kano zuwa Katsina, Ana Asarar Rayuka

  • Masu bin titin Kano-Gwarzo-Dayi sun bayyana fargaba da takaici a kan yadda aka yi watsi da aikin da aka bayar da kwangilar shekaru uku baya
  • Sun ce gwamnatin tarayya ta bayar da kwangilar shekaru da suka gabata, kuma ta hada da jihohin Katsina, Sakkwato Zamfara, Kebbi da Kano
  • Sai dai a koken jama'a, an gano yadda 'yan kwagilar suka kwashe baki daya kayan aikinsu, ballanatana a sa rai da za su dawo don karasa aikin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Direbobin da ke amfani da hanyar Kano-Gwarzo-Dayi sun ci gaba da bayyana damuwa kan lalacewar hanyar da ta zama haɗari ga rayuka da dukiyoyi.

Sun ce ’yan kwangilar da ke aikin gyaran hanyar sun bar aikin ne shekara ɗaya kacal bayan gwamnatin tarayya ta ba da kwangilar faɗaɗa hanyar zuwa hannu biyu.

Kara karanta wannan

N Power: Matasa sun tuna da Buhari, an maka Tinubu a kotu kan basukansu

Hoton ginin hanya
An tsayar da aiki titin Kano-Dayi Hoto: BanksPhotos
Source: Getty Images

A labarin da ya kebanta ga Punch News, ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ce ta kaddamar da aikin gina sabon titin daga Kano zuwa garin Dayi da ke jihar Katsina.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An bayar da aikin a kan kudi sama da N62.7bn, amma abin takaici shi ne aikin ya tsaya cak babu ci gaba.

Hanyar Kano-Gwarzo-Dayi da ke da tsawon kilomita 82.3 na hannu ɗaya ne a da, kuma gwamnati ta yi niyyar faɗaɗa ta ne domin sauƙaƙa jigilar mutane da kayayyaki a yankin.

Sai dai bincike ya nuna cewa hanyar na da matuƙar muhimmanci, domin tana haɗa Kano da wasu jihohi guda huɗu da kuma Jamhuriyar Nijar.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
An zargi gwamnati da hana yan kwangila kudinsu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Yanzu haka hanyar ta koma tarkon mutuwa, domin ’yan kwangilar da ke aikin faɗaɗa hanyar sun janye daga wurin aikin tare da kwashe kayayyakin su gaba ɗaya.

Hanyar Kano-Gwarzo-Dayi na daga cikin manyan hanyoyi da ke haɗa jihohin Katsina, Sakkwato inda ta zarce har jamhuriyyar Nijar, sai Zamfara da Kebbi da Kano.

Kara karanta wannan

Batan maciji ya birkita ƴan Kano, Sanusi II ya roƙi kwamishinan ƴan sanda alfarma

Ana zargin 'yan kwangila da watsi da aiki

Bincike ya gano cewa barin aikin da ’yan kwangilar suka yi na da alaƙa da gazawar gwamnatin tarayya wajen sakin kuɗin aikin.

Haka zalika, akwai zargin cewa gwamnati ba ta biya diyya ga manoma da masu gonaki da filaye da aka mamaye domin aikin ba.

Wani direban mota a yankin, Bala Abubakar, ya shaidawa manema labarai a ƙauyen Gude ranar Lahadi cewa direbobi da dama sun daina bin hanyar.

A cewarsa:

“Sakamakon lalacewar hanyar, an samu hadura kusan kullum, kuma hakan na janyo asarar rayuka da dukiyoyi,."

Bola Tinubu ya yi magana kan aikin titi

A wani labarin, mun wallafa cewa Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinub ya bayyana cewa za a kammala aikin titin Abuja-Kaduna-Zaria-Kano nan da watanni 14 masu zuwa.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan yayin bikin kaddamar da gyaran sashen farko na hanyar daga Abuja zuwa Kaduna.

Ya ce aikin ya kunshi buɗe titin da sake gyara shi da samar da sababbin magudanar ruwa, da kuma sanya katanga da za ta raba hanyar zuwa da dawowa a tsakiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng