Farashin Buhun Siminti Zai Karye a Najeriya, BUA Ya Hango Abin da ke Shirin Faruwa a 2025

Farashin Buhun Siminti Zai Karye a Najeriya, BUA Ya Hango Abin da ke Shirin Faruwa a 2025

  • Farashin buhun siminti zai karye a Najeriya a 2025 matuƙar Naira ta ci gaba da ƙara daraja a kasuwar hada-hadar musaya
  • Shugaban kamfanin BUA, AbdulSamad Rabiu ne ya yi wannan hasashen a taron shekara-shekara karo na tara da aka gudanar a Abuja
  • Ya ce farashin kayan samar da siminti ne ya jawo tsadarsa, yana mai cewa kayayyaki za su sauka nan ba da jimawa ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Shugaban kamfanin simintin BUA, AbdulSamad Rabiu, ya yi hasashen karyewar farashin kayayyaki, ciki har da siminti.

AbdulSamad ya bayyana cewa akwai yiwuwar farashin kowane buhun siminti ya ragu sosai nan gaba, sakamakon farfaɗowar darajar Naira da saukin farashin samarwa.

Shugaban rukunin kamfanonin BUA, AbdulSamad Rabiu.
Farashin siminta na iya karyewa a Najeriya a 2025 Hoto: BUA Cement Plc
Source: Facebook

Shugaban kamfanin BUA ya bayyana hakan ne taron shekara-shekara karo na tara na kamfanin da aka gudanar a Abuja jiya, cewar rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Tattalin daji: Shettima ya yi korafi a taron da Kwankwaso ya halarta a Aso Villa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farashin siminti zai iya sauka a 2025

AbdulSamad Rabiu ya danganta hauhawar farashin kayayyaki da matsalolin tattalin arzikin duniya, sai dai ya nuna fatan cewa abubuwa za su kyautatu nan gaba.

“Yanzu haka canjin Dala ya kusa dawowa N1,500. Amma ina da kwarin gwiwa cewa nan gaba kadan darajar Naira za ta dawo N1,200 ko kasa da haka.
"Idan hakan ta faru, farashin kayayyaki zai sauka, ba siminti kadai ba, har da sauran kayayyaki.

- inji AbdulSamad Rabiu.

Me yasa siminti ya kai kimanin N10,000?

Da yake amsa tambaya kan dalilin da ya sa buhun siminti ya kai kimanin N10,000, Rabiu ya ce hakan ya faru ne saboda tsadar samar da shi, ba wai don neman riba mai yawa ba.

"Tsadar kayan samar da siminti ce ta sa farashin ya kai kusan N10,000. Mun zuba biliyoyin Dala a kamfanin siminti a tsawon shekaru 20 zuwa 30.

Kara karanta wannan

Ana rade radin zai shiga jam'iyyar APC, an hango Kwankwaso a fadar shugaban kasa

"Samun ribar Naira biliyan N69 bayan haraji, wanda yayi daidai da kusan Dala miliyan 40, akan irin wannan jari ba wani abu ne mai yawa ba.”

Abdul Samad Rabiu ya jaddada cewa farashin makamashi shi ne babban abu da ke haifar da tsada a kamfanin siminti, hakan ya sa suka zuba jari don gina ƙaramin wajen samar da iskar gas (LNG).

"Muna kashe kudi sosai a bangaren gas. Muna son sarrafa hakan a cikin gida idan zai yiwu,” inji shi.
Buhunan siminti na kamfanin BUA.
Shugaban kamfanin BUA, AbdulSamad Rabiu ya yi hasashen karyewar farashin kayayyaki a 2025 Hoto: BUA Cement Plc
Source: UGC

Ribar da kamfanin simintin BUA ya samu a 2024

Duk da kalubalen tattalin arziki, ciki har da faduwar Darajar Naira da tsadar kayayyakin da ake bukata, kamfanin simintin BUA ya samu kyakkyawan sakamako a 2024.

Kamfanin ya samu karin kudaden shiga da kaso 90.5%, daga Naira biliyan 460 a 2023 zuwa Naira biliyan 876.5 a 2024, rahoton Bussiness Day.

Ribar da kamfanin ya samu kafin haraji ta karu da kaso 48.2% zuwa Naira biliyan 99.63 a 2024, idan aka kwatanta da Naira biliyan 67.2 biliyan a 2023.

Sai dai asarar da kamfanin ya yi saboda canjin kudi ta karu zuwa Naira biliyan 93.9 a 2024, daga Naira biliyan 69.9 a shekarar da ta gabace ta.

Kara karanta wannan

Taron APC: Tinubu ya shiga tsaka mai wuya game da zakulo magajin Ganduje

Shugaban BUA ya yabawa Bola Tinubu

A baya, kun ji cewa shugaban BUA, AbdulSamad Rabiu ya yabawa salon shugabancin Bola Ahmed Tinubu a Najeriya.

Ya ce daga zuwan shugaba Tinubu, tattalin arzikin da ya kama hanyar taɓarɓarewa ya fara farfaɗowa domin ci gaban ƙasa.

Hamshakin dan kasuwar ya sha yabon Bola Tinubu kan tsare-tsaren tattalin arziki da ya dauka a Najeriya bayan hawansa mulki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262