Tinubu Ya Yi Bayani yayin da aka Fara Taron Daidaita Farashin Fetur a Abuja
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa lokaci ya yi da Afirka za ta fitar da tsari na kanta wajen saka farashin albarkatun man fetur
- Ana gudanar da taron harkar mai a Abuja tsakanin 22 zuwa 23 ga Yuli 2025, domin ƙarfafa haɗin gwiwa a tsakanin kasashen Afirka
- Shugaban kasar ya ce Najeriya da abokan tafiyarta suna aiki domin samar da yanayin kasuwa mai inganci da aminci a fannin man da aka tace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Najeriya ta buɗe kofarta don maraba da shugabannin makamashi daga sassan Afirka da wasu abokan hulɗarta domin halartar taron makamashi a Abuja.
Taron da Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur ta Najeriya (NMDPRA) ta shirya zai mayar da hankali kan harkar man da aka tace.

Source: UGC
Legit ta tattaro bayanan da shugaba Bola Tinubu ya yi kan taron ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafin shi na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taron zai gudana ne daga ranar 22 zuwa 23 ga Yuli 2025, kuma zai tattauna batutuwa kamar tsare-tsaren farashi, daidaita ƙa'idoji da kuma tasirin kasuwar cikin gida.
Tinubu ya nemi Afirka ta kafa tsarin farashi
A bayanin da ya yi, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna cewa lokaci ya yi da kasashen Afirka za su daina zama masu karɓar farashin da kasuwannin duniya ke saka musu.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa:
“Afirka ba za ta ci gaba da zama mai karɓar farashi ba. Lokaci ya yi da za mu kafa tsari na gaskiya da bayyana gaskiyar abin da ke wakana a kasuwanninmu, wanda zai kare tattalin arzikinmu.”

Source: Facebook
'Haɗin kai da gaskiya ne mafita' – Tinubu
Ana sa ran wajen taron zai zama wata kafa ta farfado da martabar nahiyar Afrika da kuma samun damar mallakar albarkatunta.
Shugaban ya ci gaba da cewa:
“Ta hanyar wannan dandali mai muhimmanci, muna fatan kafa wata kasuwa da Afirka da kanta za ta jagoranta, mai haɗin kai da kuma ikon cin gashin kai a tattalin arziki.”
Ya bayyana hakan a matsayin wata sabuwar hanya da za a mallaki albarkatun da ake da su, a kuma samar da makoma mai kyau ga ‘yan Afirka.
Tinubu ya kammala da cewa:
“Dole ne mu saka farashi bisa abin da muke samarwa. Mu mallaki darajar albarkatunmu. Wannan shi ne yadda za mu samar da ci gaba mai ɗorewa ga nahiyarmu da ‘ya’yanta.”
Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa 'yan Najeriya za su iya bibiyan yadda taron ke gudana kai tsaye ta nan.
An yi taron tattalin daji a Abuja
A wani rahoton, kun ji cewa an gudanar da taron tattalin arzikin daji a Najeriya domin samar da sana'o'i da ayyuka ga matasa.
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettim ya bayyana cewa kasashe da dama kamar Habasha suna samar da ayyuka ta hanyar amfani da tattalin daji.
Legit ta rahoto cewa Sanata Kashim Shettima ya nuna damuwa matuka kan 'yadda ba a amfani da dajin Najeriya yadda ya kamata.
Asali: Legit.ng

