Tattalin Daji: Shettima Ya Yi Korafi a Taron da Kwankwaso Ya Halarta a Aso Villa

Tattalin Daji: Shettima Ya Yi Korafi a Taron da Kwankwaso Ya Halarta a Aso Villa

  • Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana a wajen taron tattalin arzikin dazukan Najeriya a fadar shugaban kasa
  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce Najeriya ta rasa fiye da kashi 90 na dazuka kuma tana asarar hekta 400,000 a shekara
  • A daya bangaren, kamfanin Netzence ya bayyana cewa yana amfani da fasaha domin samar da Dala biliyan 2 daga albarkatun daji a Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A ranar Litinin, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya halarci taron tattalin arzikin dazukan Najeriya da aka yi Aso Villa.

Wannan taron dai ya gudana ne a karkashin kwamitin shugaban kasa kan hada-hadar tattalin arziki na PreCEFI.

Mataimakin shugaban kasa ya yi korafi kan dazukan Najeriya
Mataimakin shugaban kasa ya yi korafi kan dazukan Najeriya. Hoto: Kashim Shettima
Source: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da kwararru kan muhalli da tattalin arziki, inda aka tattauna kan hanyoyin farfado da tattalin arzikin dazuka.

Kara karanta wannan

Ana rade radin zai shiga jam'iyyar APC, an hango Kwankwaso a fadar shugaban kasa

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da mataimakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Hadejia ya wakilta, ya bayyana irin mummunan halin da dazukan Najeriya ke ciki.

Bayanin Shettima a gaban Kwankwaso

A yayin bude taron, Mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa fiye da kashi 90 cikin 100 na dazukan Najeriya sun lalace.

Shettima ya ce Najeriya tana asarar sama da hekta 400,000 na daji a duk shekara, yana mai cewa wannan matsala ba wai ta muhalli ba ce kawai, illa ta tattalin arziki ce babba.

Punch ta wallafa cewa mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa rashin kula da albarkatun daji zai ci gaba da jefa Najeriya cikin talauci.

Najeriya na iya yin koyi da kasashe

Shettima ya bayar da misalan kasashe kamar Vietnam da ke samun fiye da dala biliyan 15 a duk shekara daga albarkatun daji, da Brazil da ke samun kashi 15 na kudinta daga dajin Amazon.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya isa fadar shugaban kasa taron da ake sa ran Tinubu zai halarta

Ya kara da cewa Habasha ta samar da ayyukan yi 350,000 ta hanyar shuka sababbin dazuka da sarrafa albarkatunsu.

A cewarsa, Najeriya ba wai kawai kamata ya yi ta koyi daga wadannan kasashe ba, ya kamata ta zama jagorar kirkire-kirkire a fannin masana'antar daji a nahiyar Afirka.

Lokacin da Kwankwaso ya isa Villa taron tattalin dazuka.
Lokacin da Kwankwaso ya isa Villa taron tattalin dazuka. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Twitter

Kira kan amfani da fasahar zamani

Mataimakin shugaban kasar ya ce Najeriya ba za ta iya cigaba da yin watsi da wannan dama ba, yana mai kira da a hada da sabbin fasahohi da kudi cikin hanyoyin rayuwa da suka danganci daji.

Shettima ya ce fiye da mutane miliyan 30 za su amfana matuka idan aka bullo da dabaru a bangaren dazukan kasar.

A nasa bangaren, wanda ya kafa kamfanin Netzence, Dr Sadiq Sani, ya bayyana cewa kamfaninsa yana da fasahar da za ta fitar da kimanin Dala biliyan 2 daga albarkatun daji na Najeriya.

Kwankwaso ya halarci taron tattali a Aso Villa

A wani rahoton, kun ji cewa an gudanar da taron tattalin daji a fadar shugaban kasa a ranar Litinin, 21 ga Yuli 2025.

Kara karanta wannan

Yadda Kiristoci suka yi wa Buhari addu'a a babban cocin kasa na Abuja

'Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP a 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya samu halartar taron.

Zuwan Rabiu Musa Kwankwaso fadar shugaban kasa ta tayar da kura musamman lura da cewa ana rade-radin cewa zai iya sauya sheka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng