Musulmi Sun Yi Babban Rashi a Najeriya, Sheikh AbdulKareem Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Musulmi sun yi rashi da Allah ya karɓi ran babban limamin garin Oruwa, Sheikh AbdulKareem Olore a jihar Oyo
- Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Oyo, Rt. Hon. Adebo Ogundoyin ya yi jimami tare da miƙa sakon ta'aziyyar rasuwar babban malamin na musulunci
- Ya ce al'ummar musulmi na Oruwa sun yi babban rashi idan aka yi la'akari da irin gudummuwar da marigayin ya bayar a rayuwarsa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Oyo - Babban limamin garin Oruwa da ke ƙaramar hukumar Ibarapa a jihar Oyo, Sheikh AbdulKareem Olore ya riga mu gidan gaskiya.
Babban malamin addinin musuluncin ya rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a garinsa na Oruwa da ke jihar Oyo a Kudu maso Yammacin Najeriya.

Source: Twitter
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Oyo, Rt. Hon. Adebo Ogundoyin, ya bayyana jimaminsa kan rasuwar babban limamin, kamar yada Tribune Nigeria ta rahoto.
Sheikh AbdulKareem Olore ya rasu
Sheikh AbdulKareem Olore ya rasu yana da shekaru 84 da haihuwa, kamar yadda bayanai suka tabbatar.
An tabbatar da rasuwarsa ne ta cikin wata sanarwar ta'aziyya da Shugaban Majalisar Dokokin Oyo, Ogundoyin ya rabawa manema labarai.
A cikin sanarwar, Rt. Hon. Ogundoyin ya bayyana marigayin a matsayin wani babban ginshiƙi, uba ga kowa, kuma jagora ga al’ummar Musulmi da ma dukkan al’ummar Eruwa.
Musulmi a Oruwa sun yu babban rashi
“Wannan babban rashi ne ga ƙasar Eruwa, da al’ummar Musulmi, kuma hakika mu da muka san Baba Sheikh AbdulKareem Olore muna daraja shi.
"Ba kawai babban limami bane, mutum ne mai ƙaunar zaman lafiya, hikima da tawali’u. Addu’o’insa, jagoranci da shawarwarinsa sun taimaka matuƙa wajen haɗin kan mutanenmu."
- In ji Rt. Hon. Adebo Ogundoyin
Ogundoyin ya tuna irin muhimmiyar rawa da marigayi Limamin ya taka wajen sasanta rikicin shugabanci da ya dade yana faruwa kan kujerar Babban Limamin Eruwa.

Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu zai halarci taron addu'a da Allah Ya karɓi rayuwar Mai Martaba Sarki
“Haƙurinsa da ƙwarewarsa a lokacin fitintinu sun ƙara nuna jajircewarsa wajen ganin an samu zaman lafiya da ci gaban al’umma da kuma tabbatar da martabar addinin Musulunci," in ji shi.

Source: Original
Kakakin Majalisar Oyo ya yi ta'aziyya
Shugaban Majalisar ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, al’ummar Musulmi na Eruwa, da kuma shugabannin addinin Musulunci a yankin Ibarapa.
Ya bukaci al'umma su ƙarfafa kansu, kuma su yi koyi da kyakkyawar rayuwar da marigayin ya yi tare da ci gaba da riƙo da halayensa na zaman lafiya, hidima da ibada.
“Baba Olore ya yi rayuwa mai kyau, yana bautawa Allah da kuma hidima ga mutane. Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta masa, ya karɓi ayyukan alherinsa, ya kuma saka masa da Aljannatul Firdaus,” in ji Ogundoyin.
Sheikh Idris Abu Sumayya ya rasu
A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Idris Adam Kumbashi wanda aka fi sani da Abu Sumayya ya riga mu gidan gaskiya a Zaria, jihar Kaduna.
An rahoto cewa Sheikh Kumbashi ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimar addini, da'awa da koyarwa lokacin da yake raye.
Tuni dai aka an gudanar da jana'izar marigayin da misalin karfe 1:30 na rana a masallacin Juma'a na dan Magaji a Zaria.
Asali: Legit.ng
