Tsadar Taki Ya Hana Noma, ana Fargabar Samun Karancin Abinci a Najeriya

Tsadar Taki Ya Hana Noma, ana Fargabar Samun Karancin Abinci a Najeriya

  • Farashin takin zamani ya haura sosai fiye da yadda yawancin manoma ke iya samu a kasuwannin cikin gida Najeriya
  • Duk da ikirarin gwamnatin tarayya na raba takin kyauta, rahotanni sun nuna cewa manoma na barin shuka masara da shinkafa gaba daya
  • Shugabannin kungiyoyin manoma sun ce idan ba a tallafa da saukaka farashi ba, matsalar rashin abinci za ta kara ta'azzara a kasar nan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rahotanni daga jihohin da ke samar da yawancin kayan amfanin gona sun tabbatar da cewa manoma na barin shuka masara da shinkafa saboda tsadar takin zamani.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke cewa ta raba takin zamani kyauta ga manoma.

Wasu manoma na aiki a gonakin su
Wasu manoma na aiki a gonakin su. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta tattauna da manoma da sauran masu ruwa da tsaki domin jin halin da suka shiga kan tsadar taki a bana.

Kara karanta wannan

'Juyin juya hali,' An kawo hanyar warware matsalolin Najeriya gaba daya

Wasu daga cikin manoman sun bayyana cewa, yanzu haka ba za su iya sayen buhun taki ba saboda hauhawar farashin sa wanda ya kai sama da N50,000 a wasu kasuwanni.

Yayin da ake fargabar karancin abinci a Najeriya, manoma da dama na komawa shuka gero, dawa, wake da kuma kayan lambu wadanda ba sa bukatar takin sosai.

Manoma sun rungumi wake da kayan lambu

Bincike ya gano cewa manoma da dama sun daina shuka masara da shinkafa suna komawa kayan lambu kamar albasa da tattasai.

Malam Hamza Adamu daga karamar hukumar Igabi a Kaduna ya ce ba zai iya ci gaba da shuka masara ba.

Ya ce:

"Ba za ka iya sayen buhun taki da kudin da za ka sayar da buhun masara ba. Kuma idan ka shuka ba tare da taki ba, to za ka gamu da matsala sosai."

Farashin taki ya haura matuka a Najeriya

Kara karanta wannan

Rasuwar Buhari: An fara cacar baki tsakanin mutanen Tinubu da Atiku

A cewar wani bincike, buhun taki nau'in Urea yanzu ya kai tsakanin N47,000 da N50,000, yayin da NPK ke kai N55,000, lamarin da ya sanya manoma da dama hakura da shuka masara.

Wani manomi, Bello Idris Dalleje, ya ce:

"Buhun Urea yanzu ya kai N50,000, amma buhun masara yana kasa da N38,000. A haka ba za ka iya samun riba ba."

Ya kara da cewa sau da dama gwamnati na cewa ta raba taki, amma:

"Ana cewa manoma hudu su raba buhu daya, wanda hakan manomi daya ke bukata a gona daya."

Kungiyar manoman masara ta koka

Shugaban kungiyar manoman masara (MAAN) reshen Jihar Kaduna, Mohammed Kabir Salihu, ya tabbatar da cewa manoma na barin shuka masara saboda tsadar taki da kuma faduwar farashi.

Ya ce:

“Yawancin manoma yanzu sun koma shuka albasa, tattasai da sauran kayan lambu saboda suna bukatar taki kadan.”

Salihu ya zargi shigo da masara daga kasashen waje da faduwar farashinta da sanya manoma shan wahala.

Gwamnan Neja yana girbe shuka a gonar gwamnati a damunar bara
Gwamnan Neja yana girbe shuka a gonar gwamnati a damunar bara. Hoto: Balogi Ibrahim
Source: Facebook

AFAN: 'Akwai barazanar karancin abinci'

Shugaban kungiyar manoma ta kasa (AFAN), Kabiru Ibrahim, ya ce tsadar taki barazana ce ga kokarin kasar wajen cimma wadatar abinci.

Kara karanta wannan

Sauya tsarin mulki: Ana son shugaban kasa ya dawo yin shekara 6 ba tazarce

Ya ce:

“Yawancin kananan manoma da ma manyan manoma na fama da tsadar taki, wanda hakan ke barazana ga samar da wadataccen abinci a Najeriya.”

Legit ta tattauna da manomi a Gombe

Wani manomi a jihar Gombe, Ibrahim Sa'id ya zantawa Legit cewa tashin farashin taki barazana ce a gare su.

Ibrahim ya ce:

"A lokacin da muka shuka masara farashin bai kai haka ba, amma yanzu buhun taki yana neman haura N60,000.
"Idan mutum bai samu kudin sayen taki ba, yana ji yana gani gonar shi za ta lalace."

'Yan China za su fara noma a Neja

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Neja ta gayyato masu zuba jari daga kasar China domin yin noma a jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamna Umaru Bago da kan shi ya jagoranci 'yan Chinan da suka zo Najeriya zuwa yankin da za su yi noma.

Gwamnatin Neja ta bayyana cewa shirin noman zai habaka tattalin jihar tare da samarwa matasa masu zaman kashe wando aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng