'Juyin Juya Hali,' An Kawo Hanyar Warware Matsalolin Najeriya Gaba Daya
- Fasto Tunde Bakare ya ce Najeriya a karan kanta ba ta da matsala, sai dai an gina kasar a bisa mummunan tsari
- Tunde Bakare nemi yin juyin juya hali na dabi’u da tsarin shugabanci ba tare da amfani da makami ko zubar da jini ba
- Faston ya zargi gwamnati da goyon bayan barayi da mummunan tsarin siyasa da ya gurgunta kasar da gaza tsayar da adalci
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Fasto Tunde Bakare ya bayyana cewa gyaran fuska ko kwaskwarima ba zai gyara Najeriya ba, domin an gina kasar ne tun farko don cutar da talakawa.
Tunde Bakare ya ce abin da kasar ke bukata shi ne juyin juya hali na dabi’u da nagartattun shugabanni.

Source: Twitter
Rahoton Arise News ya ce Bakare ya bayyana hakan ne a wani wa’azi da ya gabatar a cocinsa, da ke Legas a ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bakare ya jaddada cewa tsarin siyasar Najeriya yana cikin halaka, saboda ana tafiyar da shi ne da cin hanci, son kai, rashin adalci da zalunci.
Bakare: 'Najeriya na bukatar juyin juya hali'
Ya ce lokaci ya yi da za a yi zabi tsakanin rugujewar kasa ko kuma juyin juya hali na dabi’u da shugabanci.
A yayin wa’azin, the Guardian ta wallafa cewa Bakare ya ce:
“An tsara kasar ne tun farko don ta ruguje. Ko kadan gyaran fuska ba zai warware matsalar ba. Abin da Najeriya ke bukata shi ne sauyi gaba daya – sauyin dabi’u.”
Ya koka da yadda masu laifi ke samun mukamai yayin daake ware wadanda ke da gaskiya da rikon amana.
“Ana zubar da jini a kasar nan. Masu mulki ba su san adalci ba, sun yi nesa da gaskiya,”
In ji shi.
Bakare ba ya nufin a zubar da jini
Faston ya bayyana cewa ba yana nufin a yi tashin hankali ko amfani da makami ba ne a kan maganar juyin juya halin.
Ya ce:
“Wannan ba kira ba ne zuwa ga rikici ba, kira ne ga sauya tunani, daga mugun buri zuwa hidimar kasa.”
Ya yi kira da a samar da sababbin shugabanni masu hangen nesa, nagarta, cancanta da adalci a Najeriya.
Faston ya ce idan har babu sauyin shugabanci da tsarin dabi’u, Najeriya ba za ta taba samun ci gaba ba.

Source: Twitter
Bakare ya yi raddi wa malaman addini
Bakare ya zargi wasu malamai da barin aikinsu na fadakarwa, suna kusantar gwamnati domin neman jin dadi.
Ya nemi Kiristoci da sauran mabiya addinai su jagoranci juyin dabi’un da kasar ke bukata:
“Har sai mun daidaita dabi’unmu da gaskiya, adalci da rikon amana, babu wani kundin tsarin mulki ko zabe da zai ceto mu.”
An bukaci sauya tsarin mulkin Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyoyin fararen hula a jihohi da dama sun koka kan yadda harkar gwamnati ke tafiya a Najeriya.
Kungiyoyin sun bukaci sauya kundin tsarin shugabanci domin rage yadda ake kashe kudi wajen kamfen da sauransu.
Sun bukaci a dawo da shugaban kasa da gwamnoni yin shekara 6 a kan mulki ba tare da yin tazarce ba domin ba su damar yin ayyuka.
Asali: Legit.ng


