Yanzu Yanzu: An kama mutum 30 yayinda ake zanga-zangar juyin-juya-hali a Lagas
- A yanzu haka daruruwan masu zanga-zanga na nan suna gangami a unguwannin jihar Lagas
- An kama mutum 30 daga ciki masu zanga-zangar a kan tabarbarewar shugabanci a Najeriya
- Suna adawa da manufofin gwamnatin Muhammadu Buhari wanda suka ce ya sanya al'umman kasar a cikin mawuyacin hali
Daruruwan masu zanga-zanga a ranar Alhamis, 1 ga watan Oktoba, sun mamaye unguwannin jihar Lagas domin nuna rashin jin dadinsu a kan tabarbarewar shugabanci a Najeriya.
Masu zanga-zangan sun yi tattaki daga unguwannin Ojota zuwa Maryland a Lagas. An gano su suna wake-wake.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa jami’an tsaro sun kama masu zanga-zangar akalla su 30.
Gamayyar masu zanga-zangar na juyin-juya hali a cikin wata sanarwa da suka saki kafin zanga-zangar, sun yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi murabus.
KU KARANTA KUMA: Tabarbarewar Najeriya: Buhari ya dora laifi a kan Obasanjo, Yar'Adua da Jonathan
Jawabin ya zo kamar haka: “Kungiyar juyin juya hali na kira ga dukkanin yan Najeriya a gida da waje da su fito kwansu da kwarkwata a ranar 1 ga watan Oktoba, domin shiga sahun zanga-zangar lumana da za a yi don neman a janye manufofin gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari na kuntatawa mutane.
“Wadannan manufofi masu tsanani da suka sanya takunkumi a aljihun mutanen Najeriya na zuwa ne a lokacin da yan kasar ke farfadowa daga matsin annobar korona, lamarin da ya taba duniya baki daya, wanda kuma gwamnatin Buhari bata yi wa riko mai kyau ba, inda a yanzu ake sake fadawa matsalolin kudi. "
KU KARANTA KUMA: Jawabin Buhari: A gani a kasa ya fi fadi da fatar baki, In ji Jega
A wani labarin, a ranar Alhamis, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa kasar nan tana cikin mawuyacin hali a fannin tattalin arziki.
Ya ce hakan kuwa daidai yake da kowacce kasa domin kuwa dukkan duniya ne ake cikin wannan halin.
Buhari ya sanar da hakan ne a jawabinsa ga 'yan Najeriya a ranar da kasar ta cika shekaru 60 da samun 'yancin kai.
Shugaban kasar ya kara da amincewa da cewa, kasar na fuskantar matsalolin tsaro daban-daban a sassan kasar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng