Awujale: Yadda Basarake Ya Assasa Kafa APC, Nasarar Buhari a 2015
- Fasto Tunde Bakare ya tuno yadda aka kafa jam'iyyar APC har ta samu nasara a babban zaɓen shekarar 2015
- Malamin addinin ya bayyana cewa Awujale na Ijebu, marigayi Oba Sikiru Adetona ya assasa kafa jam'iyyar APC
- Ya bayyana cewa da ba don rawar ganin da basaraken ya taka ba, da ba a samar da jam'iyyar APC ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Fasto Tunde Bakare, babban mai kula da Cocin Global Community Citadel, ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa yadda gwamnatin sa ta shirya jana’izar marigayi Muhammadu Buhari.
Haka kuma, ya yi gagarumar jinjina ga Awujale na Ijebuland, Oba Sikiru Adetona, wanda shi ma ya rasu a rana ɗaya da marigayi Buhari.

Source: Twitter
Fasto Tunde Bakare ya bayyana haka ne yayin jawabinsa na “halin da ƙasa ke ciki” a ranar Lahadi a dakin taron cocin, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Fasto Bakare, rasuwar waɗannan mutane biyu a rana ɗaya wani iko ne na ubangiji.
Yadda Awujale ya taka rawar kafa APC
Ya tuna cewa, ko da yake Awujale ba ɗan siyasa ba ne, amma ya taka rawa sosai wajen haɗa jam’iyyun adawa waje guda, wanda hakan ya haifar da jam’iyyar APC inda har ya kai ga nasarar Buhari a zaɓen 2015.
Ya bayyana yadda ya tunkari Awujale don ya roƙi Tinubu da ya jagoranci batun haɗewar jam’iyyun, wanda ya amince da hakan.
Fasto Bakare ya ƙara da cewa, da marigayi sarkin wanda ya rasu yana da shekara 92 bai shiga tsakani wajen wannan haɗin gwiwa ba, da kuwa APC ba ta samu ba.
"Ba tare da rawar ganin da Awujale ya taka ba, da APC ba za ta samu a matsayin jam’iyya ba."
"Mai martaba (Kabiyesi) ne ya kira wani muhimmin taro a otal ɗin Oriental da ke Victoria Island, inda aka cimma matsaya wacce ta haifar da kafuwar jam’iyyar APC."
"Duk da hakan, Kabiyesi bai tsaya ga wata jam’iyya ba, yana goyon bayan duk wani yunƙuri da yake ganin zai kawo nagartaccen mulki, ya ƙarfafa muradun ƙasa, ya bunƙasa zaman lafiya, da kuma gina Najeriya ɗaya.”
“Har zuwa lokacin rasuwarsa, ya kasance dattijo nagari, ɗan ƙasa na gari, mai ba da shawara, aboki na gaske, kuma wata baiwar Allah ga ƙasarmu."
- Fasto Tunde Bakare

Source: Twitter
Fasto Bakare ya magantu kan kafa APC
Fasto Bakare ya jaddada cewa haɗakar da aka yi da ta haifar da APC shi ne karon farko da masu kishi daga Arewacin Najeriya da na Kudancin Najeriya suka haɗa hannu waje guda, wani abu da ba a taɓa samu ba a baya.
Ya ce rasuwar waɗannan mutane biyu manya na nuna wata alama ce ta samun sauyi, wanda ƴan kaɗan ne kawai za su iya fahimta.
Sanata Binani ta fice daga APC zuwa ADC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsoguwar ƴar takarar gwamnan jihar Adamawa, Sanata Aishatu Binani ta fice daga jam'iyyar.
Sanata Binani wacce ta taɓa wakiltar Adamawa ta Tsakiya a majalisar dattawa ta koma jam'iyyar haɗaka ta ADC.
Ta bayyana cewa za su yi tafiya a cikin ADC wacce ke ci gaba da samun manyan ƴan siyasa da suke komawa cikinta.
Asali: Legit.ng

