"Ina Wutar da Ka Yi Alkawari?": ADC Ta Jefawa Tinubu Tambaya da Ya Kamata Ya Amsa
- Jam’iyyar ADC ta zargi Shugaba Bola Tinubu da gaza cika alkawarin da ya dauka na samar da wutar lantarki ba tare da katsewa ba
- Ta bayyana cewa hauhawar farashin wuta da yawan durkushewar tashar wutar ya jefa miliyoyin ‘yan Najeriya cikin duhu
- Jam’iyyar ta ce rabin wa’adin mulkin Tinubu ya wuce ba tare da wani ci gaba ba, inda ta ce 2027 za su hukunta gwamnatin da kuri’a
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Jam’iyyar ADC ta ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gaza cika alkawarin yakin neman zabe na samar da wutar lantarki ba tare da katsewa ba cikin shekaru hudu.
ADC ta zargi gwamnatin Tinubu da jawo tabarbarewar harkar wutar lantarki, duk da karin kudin wuta da kuma wahalhalun rayuwa da jama’a ke fuskanta.

Source: Twitter
ADC ta kalubalanci Tinubu kan wutar lantarki
Sakataren yada labarai na kasa na jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X da safiyar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam’iyyar ADC ta ce bayan fiye da shekaru biyu da fara mulkin Tinubu, babu wani ci gaban azo-a-gani da aka samu a bangaren samar da lantarki.
Maimaikon haka, ADC ta ce ‘yan Najeriya sun kara ganin hauhawar kudin wuta, durkushewar tushen wuta akai-akai da rashin wadatacciyar wuta, musamman a yankunan karkara.
Jam’iyyar ta bukaci shugaban kasa da ya fadi dalilin da yasa har yanzu miliyoyin ‘yan kasa ke zaune cikin duhu duk da alkawuran da ya yi a baya.
ADC ta tunawa Tinubu alkawarinsa na 2023
Sanarwar Bolaji Abdullahi ta ce:
“Yau muna so mu tunatar da Shugaba Tinubu cewa ya yi wa ‘yan Najeriya alkawarin samar da wutar lantarki ba tare da katsewa ba cikin shekaru hudu.
"Eh, da bakinsa, ya ce zai samar da wutar lantarki ta awanni 24 a kowacce rana. Amma yau, wannan alkawarin ne mafi muni wajen gaza cikawa."
Game da wannan matsala, ADC ta fadi hanyoyi uku da rashin cika alkawarin Tinubu ya shafi kasar:
"1. Tun lokacin da Tinubu ya hau mulki, an kara kudin lantarki da kashi 240, amma tushen wuta ya fadi sau 12, lamarin da ya jefa miliyoyin mutane da kamfanoni cikin duhu.
"2. Har yanzu, akwai sama da ‘yan Najeriya miliyan 90 da ba su da lantarki, kuma da yawa daga masu samun wutar ba ta wuce ta awa 4 zuwa 6 a rana a karkashin tsarin Band A–E .
"3. A karkara, mafi yawan iyalai miliyan 50 na kasar nan suna rayuwa ba tare da akwai kyayyakin kai masu wutar lantarki ba – ba su da alamar wuta ko kadan."

Source: Twitter
ADC ta fadi abin da ke jiran Tinubu a 2027
Duk da wadannan matsaloli da ta ce suna faruwa, jam'iyyar ADC ta kuma ce:
“Har yanzu shugaban kasar bai dauki matakin da ya dace ba. A cikin watanni 26, babu sauyin da aka gani, babu tsare-tsare masu ma’ana.
“Mun riga mun kai rabin wa’adin wannan gwamnati, amma miliyoyin mutane na cigaba da cajin waya a shagunan cajin waya na kudi, suna kashe dubban nairori wajen sayen mai domin amfani da janareto.
“Don haka, Shugaban kasa, a wannan safiyar Lahadi, muna tambaya: Ina wutar? Me ya faru da alkawarin da ka yi?
"Kuma har yaushe ne ‘yan Najeriya za su ci gaba da zama a cikin duhu?
“Ka taba cewa: ‘Idan ban kawo muku lantarki ba, kada ku sake zaba ta.’ To, ‘yan Najeriya sun ji. Kuma a 2027, zamu cika maka wannan buri naka.”
'Yan Najeriya sun fusata kan wutar lantarki
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan Najeriya da dama sun mamaye kafafen sada zumunta domin nuna bacin ransu kan sake durkushewar tashar wutar lantarki.
An ruwaito cewa, tashar wutar lantarkin ta sake lalacewa a karo na biyu cikin kwanaki uku, lamarin da ya jefa mutane a cikin duhu.
Bayan sanarwar durkushewar tashar da gwamnati ta fitar, Legit Hausa ta zanta da wasu 'yan Arewa, suka aika sako ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Legit.ng


