UNIMAID: An Ki Yarda Tinubu Ya Sauya Sunan Jami'ar Maiduguri zuwa Muhammadu Buhari

UNIMAID: An Ki Yarda Tinubu Ya Sauya Sunan Jami'ar Maiduguri zuwa Muhammadu Buhari

  • Dalibai da kungiyar Alumni sun bayyana rashin amincewarsu da sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Jami’ar Muhammadu Buhari
  • Sun bayyana cewa UNIMAID alama ce ta juriya, ilimi da adabin gargajiya, la’akari da yadda ta tsira daga rikicin tsaro a Arewa maso Gabas
  • Sun ba da shawarar a sauya sunan jami’ar sufuri ta Daura ko jami’ar sojoji ta Biu sabanin lalata martabar UNIMAID don karrama Buhari

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Maiduguri - Tsofaffin dalibai (Alumni) da ma wadanda ke karatu yanzu a jami’ar Maiduguri da wasu ’yan jihar Borno sun aika sako ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A cikin takardar korafin da suka rubuta, sun nuna adawa da matakin Tinubu na sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Jami’ar Muhammadu Buhari domin girmama marigayin.

Daliban yanzu da na da na jami'ar Maiduguri sun ki yarda Tinubu ya sauya sunan UNIMAID zuwa Buhari
Babbar shiga kofar jami'ar UNIMAID da Tinubu ya mayar da ita jami'ar Muhammadu Buhari. Hoto: @uni_maid
Source: Twitter

An nuna kin amicewa da sauya sunan UNIMAID

Kara karanta wannan

Yobe: Sarki ya tara malamai, sarakuna domin addu'o'i na musamman ga Buhari

Channels TV ta rahoto daliban yanzu da tsofaffin daliban jami’ar UNIMAID da wasu masu ruwa da tsaki a Borno sun bayyana cewa Jami’ar Maiduguri ta wuce matsayin suna kawai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun ce jami'ar UNIMAID wata alama ce ta juriya, ƙwarewar ilimi, da al'adun gargajiya, musamman la’akari da yadda ta tsira daga ƙalubalen tsaro da yankin Arewa maso Gabas ya fuskanta a baya.

Don haka, sun fadawa Shugaba Tinubu cewa ya fi dacewa ya sauya sunan jami’ar sufuri ta tarayya da ke Daura ko kuma jami’ar sojoji ta Biu zuwa Jami'ar Muhammadu Buhari, kasancewar su na da alaƙa da tarihi da asalinsa na soja.

An bukaci jama'a sun sanya hannu don nuna goyon baya kan wannan korafi, kuma zuwa yanzu, sama da mutane 9,000 ne suka sanya hannu cikin awa 48 da suka wuce.

Korafin da aka aikawa Shugaba Tinubu

Ga yadda takardar ƙorafin ta kunshi bayanin dalilai:

“Mu, tsofaffin dalibai, dalibai na yanzu, da sauran masu kishin ƙasa, muna roƙon Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya sake duba wannan mataki da ya ɗauka na sauya sunan Jami’ar Maiduguri zuwa Jami'ar Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

UNIMAID: An faɗi babban dalilin da ya sa Tinubu ya sauya sunan jami'a saboda Buhari

“Duk da girmamawa da muke da ita ga marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, mun yarda cewa wannan sauyin suna ba ya wakiltar ra’ayoyin masu ruwa da tsaki na jami’ar da kuma martabar da ta gina ta tun shekaru aru-aru.
“Jami’ar Maiduguri ta fi karfin suna; alama ce ta juriya, kwarewa a ilimi da kuma al’adun yankin, musamman a lokacin da ta tsaya da ƙarfinta wajen fuskantar barazanar tsaro da ta addabi yankin Arewa maso Gabas.
“Sunan Jami’ar Maiduguri yana da zurfin ma’ana ga jama’ar da take bauta wa, kuma yana wakiltar muhimmiyar rawa da jami’ar ke takawa wajen cigaban ƙasa, samar da zaman lafiya da haɓaka tunanin ilimi a Arewacin Najeriya.”
An nemi Tinubu ya sauya sunan jami'ar zirga-zirga ta Daura zuwa sunan Buhari
An aika sakon korafi ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan sauya sunan UNIMAID. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Rokon da aka yiwa Tinubu kan UNIMAID

Sun ci gaba da cewa:

“Fiye da shekaru 40, wannan jami’a ta samar da shugabanni, masana, jakadu, masana kimiyya da masu kishin ƙasa da ke alfahari da kasancewarsu tsofaffin daliban UNIMAID.
“Muna roƙon Shugaba Tinubu da ya janye wannan mataki. A maimakon haka, ya girmama sunan Muhammadu Buhari ta hanyar sauya sunan wani gini ko cibiyar bincike ko wani babban aiki na ci gaba – amma ba ta hanyar lalata tarihin jami’ar Maiduguri ba.

Kara karanta wannan

Malaman Musulunci da Kiristoci sun taru a Daura, an hadu don roka wa Buhari rahama

“Muna bada shawarar cewa jami’ar sufuri ta Daura, inda Buhari ya fito, ta dace da wannan sauyin suna – don tana da alaƙa da asalinsa da yankin.
“Bugu da ƙari, kasancewarsa tsohon janar na soja, jami’ar Sojoji da ke Biu ita ma ta fi dacewa a sauya mata suna, domin tana nuna tarihin sojanci da jagorancin da Buhari ya yi.
“Wannan ƙorafi ba ra’ayin siyasa ba ne – illa kira ne don a ci gaba da mutunta tarihin jami’ar UNIMAID da kuma alakar da mutane ke da ita da sunan.”

Tinubu ya sauya sunan UNIMAID zuwa Buhari

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami’ar Maiduguri zuwa 'Jami'ar Muhammadu Buhari', a matsayin girmamawa.

Tinubu ya ce Buhari mutum ne mai gaskiya da rikon amana, wanda bai yarda da son rai ko tafiye-tafiyen siyasa marasa tushe ba.

Shugaban ya bayyana cewa Buhari ya kafa tsari na gaskiya da rikon gaskiya da zai ci gaba da zama madubi ga shugabannin gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com