Shugaba Buhari zai bude Jami’ar Sojojin da aka gina a Garin Biu cikin Jihar Borno
Mun samu labari cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai bude katafairyar Jami’ar Sojojin da aka gina a Kudancin Jihar Borno. A ranar Talata mai zuwa ne aka shirya kaddamar da katafariyar Makaranta.
Rundunar Sojin Najeriya ta bakin Jami’in ta Birgediya Janar Texas Chukwu bayyana cewa za ta bude Jami’ar da ta gina a Garin Biu da ke Jihar Borno inda kuma za a fara daukan Dalibai domin zangon karatu na shekaran 2018 da 2019.
Shugaban Kasa Buhari da kan sa ne zai zama babban bako na musamman a wajen bude Jami’ar. Za a yi wannan biki ne a farfajiyar sabuwar Jami’ar da ke cikin Garin Biu kamar yadda Darektan yada labarai na gidan Sojin kasar ya bayyana.
Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari dai ta ware makudan kudi har sama da Naira Biliyan 2 wajen gina wannan Jami’ar. Shugaban Hafsun Sojan Najeriya Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai yayi ruwa da tsaki wajen wannan aiki.
KU KARANTA: Buhari ya isa Garin Fatakwal domin kaddamar da wasu ayyuka
Yanzu dai mun samu labari cewa za a kaddamar da wadannan motocin da Sojojin Najeriya su ka kera a karshen makon nan. Shugaban Hafsun Sojin kasa Laftanan Janar Tukur Yusuf Buratai shi ne zai kaddamar da wadannan tan-tan.
Gwamnati ta cika alwashin da tayi domin tuni Janar Tukur Buratai dama yayi alkawarin za a bude Jami’ar a wannan shekaran inda yace sabuwar Makarantar za ta kunshi Jami’an Sojojin Najeriya da kuma sauran Jama’an Gari masu farar hula.
Dazu kun ji cewa wasu dakarun Sojojin Kasar nan da ke Makarantar kananan Sojoji ta Zaria sun kera wasu motoci na musamman na fita yaki da hannun tare da hadin gwiwar Jami’ar nan ta ABU Zaria.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng