Tanka Makare da Fetur Ta Yi Hatsari, Ta Kama da Wuta kusa da Gidan Man NNPCL
- Wata tanka maƙare da fetur ta yi bindiga a yankin Celica da ke Ibadan, inda gobara mai ƙarfi ta tashi da misalin ƙarfe 6:30 na yamma
- Ma’aikatan kashe gobara daga jiha da tarayya sun shawo kan wutar cikin lokaci, inda suka hana ta bazuwa zuwa gidan man NNPC
- An ce shanyewar birki ne ya haddasa hatsarin, inda tankar ta yi karo da wata mota ƙirar Prado, amma babu asarar rai sai motoci da suka ƙone
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Oyo - Wani mummunan fashewar tanka ya faru a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, yayin da wata tanka ɗauke da man fetur ta yi karo da wata motar haya.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:30 na yammacin Alhamis, 17 ga Yuli, 2025, a unguwar Celica kusa da Adegbayi, kan sabon titin Ife, a Ibadan.

Source: Twitter
Tanka makare da mai ta fashe a Oyo
Shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Oyo, Akinyinka Akinyemi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, inji rahoton Channels TV.
“A gaggauce tawagar ma’aikatan kashe gobara ƙarƙashin jagorancin ACFS Adeniyi Adesina suka garzaya zuwa inda lamarin ya faru,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa:
“Da suka isa, sun tarar da wata tanka dauke da lita 33,000 na man fetur ta yi bindiga, ita da wata motar haya suna ci da wuta.
“Ma’aikatan kashe gobarar sun shawo kan wutar da sinadarin kumfa don hana yaduwar gobarar zuwa gidan mai na NNPC da sauran gine-ginen da ke kusa."
Abin da ake zargin ya jawo hasalin
Rahoton Punch ya bayyana cewa jami’an hukumar kashe gobara ta tarayya da ta jiha ne tare suka yi nasarar kashe wutar.
Bincike na farko ya nuna cewa gobarar ta samo asali ne daga tangarda a birkin tankar man yayin da take tafiya.
An ce shanyewar birkin ya sa tankar ta kwace a hannun direban, ta yi karo da wata motar Prado da wata karamar mota, kafin ta kife a fili ta kama da wuta.

Source: Original
Asarar da aka yi a fashewar tankar
Ba a samu asarar rai ba, sai dai tankar da wata motar haya da ke wajen sun ƙone, yayin da motar Prado ɗin ta fada cikin wata rijiya kusa da inda lamarin ya faru.
An bayyana cewa gidan man kamfanin NNPC da sauran gine-ginen da ke kusa sun tsira daga gobarar bisa taimakon gaggawa na jami’an kashe gobara.
An kashe gobarar gaba daya da misalin ƙarfe 10:00 na daren ranar Alhamis, sannan an maido da doka da oda ta hanyar haɗin gwiwar ’yan sanda, NSCDC, Amotekun da jami’an kula da zirga-zirga.
Tankar man fetur ta fashe a jihar Neja
A wani labarin, mun ruwaito cewa, an samu tashin gobara bayan wata tankar mai ɗauke da man fetur ta tashi a wani gidan mai da ke jihar Neja.
Lamarin ya auku ne garin Kontagora lokacin da ke sauke fetur daga cikin tankar a yammacin ranar Lahadi, 23 ga watan Maris 2025.
Kwamandan hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) ya bayyana namijin ƙoƙarin da jami'ansa suka yi wajen shawo kan gobarar da ta tashi.
Asali: Legit.ng

