London Clinic: An Gano Makudan Kudi da Ake Biya Kullum a Asibitin da Buhari Ya Rasu
- Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rasu a asibitin London bayan ya kwanta rashin lafiya duk da cewa an shirya sallamarsa ranar
- Asibitin da Buhari ya mutu ya na cikin mafi tsada a Burtaniya, inda ake biyan har £3,500 (N7m) kullum a dakin ICU
- Dan uwansa Mamman Daura, Buhari yana cikin koshin lafiya ranar Asabar kafin ya fuskanci matsananciyar numfashi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
London, Britain - Asibitin London a Birtaniya ya ja hankalin jama’a bayan rasuwar tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya rasu.
Tsohon shugaban kasar ya rasu a asibitin London a ranar Lahadi 13 ga watan Yulin 2025 da ta gabata.

Source: Twitter
Bayanai kan asibitin London da Buhari ya rasu
Rahoton Punch ya ce Buhari da tsohon shugaban kasa Abdulsalami Abubakar dukkansu sun kwanta a asibitin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar dan uwansa Mamman Daura, Buhari yana cikin koshin lafiya ranar Asabar kafin ya fuskanci matsananciyar numfashi a rana Lahadi da rana.
Ya ce:
“Ina tare da shi zuwa 9 na dare Asabar, ya ce zai yi ganawar da likitansa ranar Lahadi, amma ya fara fama da numfashi."
Buhari ya tafi Birtaniya tun watan Afrilu domin duba lafiyarsa, daga bisani sai ya kamu da rashin lafiya mai tsanani, sai ya shiga ICU.
Menene silar mutuwar Buhari a asibitin London?
Ba a bayyana dalilin mutuwarsa ba, amma an san ya shafe shekaru da dama yana fama da ciwon lafiya kafin rasuwarsa.
Asibitin yana da gado 13 na ICU, dakin tiyata 10, cibiyoyin cutar daji guda 5 da likitoci da masu jinya sama da 900.
Fannonin da asibitin ke da kwarewa sun hada da tiyatar kashi, tiyatar ciki, tiyatar ido, tiyatar ENT da kuma tiyatar kwakwalwa.

Source: Facebook
Buhari: Makudan kudi da ake biya a asibitin London
Rahoton asibitin London na 2021 ya nuna suna duba marasa lafiya sama da 120,000 a duk shekara daga sassa daban-daban na duniya.
Wani likita dan Najeriya da ke aiki a Birtaniya ya ce asibitin na da kayan aiki masu inganci da kwararrun ma’aikata da manyan abokan hulɗa.
Ya ce ana biyan £100 zuwa £750 a kowane ganawa da likita, sannan tiyata na kai £10,000 zuwa £13,000 bisa wahalar lamarin, cewar rahoton FIJ.
Ya kara da cewa ɗakin kwana na yau da kullum na kai £1,000 zuwa £1,800, kwana a dakin ICU na kai £3,000 zuwa £3,500 kimanin N7m kenan.
Wani bincike na NIH ya ce dakin kwana na gama gari a asibitin na kai £586.59 a kowace rana, baya ga sauran kudaden magani.
Majalisar Dinkin Duniya ta jajantawa Buhari
Kun ji cewa sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya jajanta wa Najeriya kan rasuwar Muhammadu Buhari, yana yabawa da rawar da ya taka .
Guterres ya ce Buhari ya tsaya tsayin daka wajen samar da zaman lafiya a Afirka, kuma ya goyi bayan cigaban duniya da Majalisar Dinkin Duniya.
Jakadan Najeriya ya ce ziyarar Guterres ta nuna irin darajar Buhari a duniya, musamman matsayin da ya ke da shi a Afirka.
Asali: Legit.ng

