'Babu Kuɗi': Yadda Buhari Ya Roƙi Gwamnoni Su Tara N700m kafin Ya Biya Su daga Baya

'Babu Kuɗi': Yadda Buhari Ya Roƙi Gwamnoni Su Tara N700m kafin Ya Biya Su daga Baya

  • Ministan tsare-tsaren kasafin kudi, Sanata Atiku Bagudu, ya ce Muhammadu Buhari ya rayu da tawali’u da gaskiya
  • Bagudu ya ba da misalai na tawali’un Buhari, ciki har da yadda ya ki amfani da ayari a jana’izar abokinsa kafin zabe na 2015
  • Ya bayyana yadda Buhari ya fuskanci matsalolin tsaro da tattalin arziki da gaskiya, ya taimaki jihohi da basu iya biyan albashi ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Ministan tsare-tsaren kasafin kudi, Sanata Atiku Bagudu ya yaba da rayuwar Muhammadu Buhari.

Bagudu ya ce tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rayu da tawali’u da gaskiya.

Minista ya yabawa rayuwar Buhari a baya
Atiku Bagudu ya kwarara yabo ga Buhari. Hoto: @Buharisallau1.
Source: Twitter

Yadda Buhari ya goyi bayan Tinubu

Ministan ya bayyana haka cikin wata gaisuwa da ya gabatar yayin zaman musamman na majalisar zartarwa wanda Buhari Sallau ya wallafa a X.

Kara karanta wannan

"Ina kewarsa," Tinubu ya faɗi alaƙarsa da Ɗantata yayin ta'aziyya a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa marigayin ya dauki shugaban kasa Bola Tinubu a matsayin dan uwa, inda ya ba da cikakken goyon bayansa a zaben 2023.

Ya ce:

"Shugaba Muhammadu Buhari ya rayu da tawali’u, gaskiya da kuma tsantsar manufa."

Bagudu ya ce kasancewarsa gwamnan Kebbi da shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC ya sa ya samu kusanci da Buhari sosai.

'Alherin Buhari kafin ya rasu' - Atiku Bagudu

Ya kawo misali da yadda Buhari ya je jana’izar abokinsa Kanal Bello Kaliel kwanaki goma kafin zabe cikin mota uku kawai ba tare da ayari ba.

Ya ce ko da labari ya karade cewa Buhari ya je Kebbi, mutane sun fito amma ya ki bude gilashin motarsa saboda girmama lamarin.

Ya kara da cewa akwai jihohi 27 da ba sa iya biyan albashi, inda Buhari ya kirkiri hanyoyi don su samu kudi su biya ma’aikata.

"A kan gabatar da dukkan batutuwan tattalin arziki a fili tare da tattaunawa, duk lokacin da ba a biya albashi ba yana nuna damuwarsa, kuma sai ya nemi mafita."

Kara karanta wannan

UNIMAID: An faɗi babban dalilin da ya sa Tinubu ya sauya sunan jami'a saboda Buhari

- Inji Bagudu.

Minista ya fadi yadda Buhari ke damuwa kan rashin albashi
Atiku Abubakar ya tuno abin alheri da Buhari ya yi. Horo: Muhammadu Buhari.
Source: Facebook

Yadda Buhari ya roki gwamnoni kuɗi

Bagudu ya ce duk da matsin tattalin arziki, Buhari ya fuskanci matsalolin tsaro da gaskiya da jajircewa.

Tsohon gwamnan Kebbi ya tabbatar da cewa Buhari ya ce babu kudi, inda ya bukaci su hada kudin sannan daga baya zai mayar da su.

Ya kara da cewa:

"Na tuna lokacin da gwamnoni bakwai suka gana da shi game da tsaro, muka tsara kasafin Naira miliyan 700 don ayyukan tsaro."

Bagudu ya ce wasu gwamnoni sun nemi a sauya hafsoshin tsaro saboda fushin jama’a, amma Buhari ya ce bai ba su kayan aiki ba.

Ya ce Buhari bai yarda a sauya su ba saboda dalilan da ba su shafi rashin aikinsu ba, yana nuna mutuncinsa.

Sarkin Damaturu ya jagoranci addu'o'i ga Buhari

Kun ji cewa Sarkin Damaturu, Alhaji Shehu Hashimi II, ya tara manyan kasa da malamai domin addu'a ga Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

'Bai mutunta kakana haka ba': Jikan Shehu Shagari bai ji dadin abin da Buhari ya yi a 2018 ba

Sarkin ya jagoranci addu’o’in musamman domin rokon gafara da rahamar Allah ga marigayi Buhari da ya rasu a London.

Dubban malamai, masu mukaman gargajiya da al’umma sun halarci taron da aka shirya domin mutunta Buhari da kuma karrama shi da addu’o’i.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.