Najeriya Ta Girma: An Gwada Jirage Marasa Matuka da aka Hada a Zariya

Najeriya Ta Girma: An Gwada Jirage Marasa Matuka da aka Hada a Zariya

  • Cibiyar fasahar sufuri ta ƙasa (NITT), Zariya, ta gudanar da gwajin farko na jiragen sama marasa matuki da injiniyoyinta suka ƙera a gida
  • Shugaban NITT, Dr Bayero Salih Farah, ya bayyana jin daɗinsa da gwajin, yana mai cewa mataki ne mai kyau wajen bunkasa fasahar sufuri
  • An gudanar da gwajin ne a hedikwatar NITT da ke Zariya, inda aka nuna yadda jiragen za su iya sauƙaƙa harkokin sufuri da sauya tsarin jigila a ƙasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna – Cibiyar fasahar sufuri (NITT) ta ɗauki babban mataki a cigaban kirkire-kirkire, inda ta gudanar da gwajin farko na jiragen sama marasa matuka da injiniyoyinta suka ƙera.

An gudanar da wannan gagarumin gwaji ne a cibiyar NITT da ke Zariya, inda aka nuna irin gudunmawar da wannan fasaha za ta iya bayarwa wajen sauya tsarin sufuri da harkokin jigila.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta ƙara fitowa, an ji babban abin da ya hana Buhari korar wasu ministoci a mulkinsa

An gwada jirage marasa matuka a Zariya
An gwada jirage marasa matuka a Zariya. Hoto: @nittzar
Source: Twitter

Bayanin da NITT ta wallafa a X ya nuna cewa shugabanta, Dr Bayero Salih Farah, ya halarci gwajin kuma ya bayyana jin daɗinsa da yadda jiragen suka yi aiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dr Bayero Salih Farah ya yi magana yana mai bayyana gwajin a matsayin nasara babba ga fasahar cikin gida.

Bayero Farah ya yaba da nasarar gwajin

Shugaban cibiyar, Dr Bayero Salih Farah, ya ce wannan gwaji shi ne mataki na farko na cusa fasahar jiragen sama marasa matuki a harkokin sufuri na ƙasa.

Daily Trust ta wallafa cewa ya ce:

“Wannan dai mataki ne na farko. Muna fatan NITT za ta jagoranci amfani da wannan fasaha a tsarin sufuri na ƙasa.”

Ya nanata kudirin cibiyar wajen ƙarfafa kirkire-kirkire, yana mai cewa abin da ke motsa duniya gaba shi ne fasaha, don haka Najeriya na da bukatar amfani da ƙwararrunta kan hakan.

Muhimmancin jirage marasa matuka

Kara karanta wannan

Sauya tsarin mulki: Ana son shugaban kasa ya dawo yin shekara 6 ba tazarce

Daraktan cibiyar fasahar sufuri, Dr. Joshua Odeleye, ya ce fasahar jiragen sama na da matuƙar muhimmanci wajen inganta tsarin sufuri na zamani.

Ya bayyana cewa jiragen za su iya sauƙaƙa jigilar kaya, rage hayaƙi mai gurbata yanayi, da kuma samar da mafita kan sufuri mai inganci da aminci.

Wani jirgi maras matuki a sararin samaniya
Wani jirgi maras matuki a sararin samaniya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Dalilin gwada jirage marasa matuka a Zariya

Dr. Odeleye ya ƙara da cewa wannan gwaji na cikin matakan da NITT ke ɗauka domin inganta bincike da kirkire-kirkire a sashen sufuri na Najeriya.

Ya ce cibiyar za ta ci gaba da jajircewa wajen cusa sababbin fasahohi a tsarin sufuri domin bunƙasa tattalin arzikin ƙasa da inganta rayuwar jama’a.

Ana fatan Najeriya za ta cigaba da amfani da fasaha da kimiyya wajen kawo cigaba a fannonin da suke jan ragamar duniya a yau.

An sa wa cibiyar fasaha sunan Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta amince da sanya wa cibiyar fasahar zamani da hukumar shige da fice sunan Bola Tinubu.

Hukumar shige da ficen Najeriya ta sabunta cibiyar ne domin saukaka harkokin sufuri wajen amfani da fasahar zamani a Najeriya.

Hakan na zuwa ne bayan an sanya wa wurare daban daban sunan shugaba Bola Ahmed Tinubu tun bayan fara mulki a 2023.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng