"Ina Kewarsa," Tinubu Ya Fadi Alaƙarsa da Ɗantata yayin Ta'aziyya a Kano

"Ina Kewarsa," Tinubu Ya Fadi Alaƙarsa da Ɗantata yayin Ta'aziyya a Kano

  • Shugaba Bola Tinubu ya isa Kano domin yin ta'aziyyar Alhaji Aminu Dantata, bayan kammala jana’izar Muhammadu Buhari a Daura
  • Tinubu ya bayyana marigayi Aminu Dantata a matsayin gwarzo, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen taimakon al’ummar Najeriya
  • Dubbannin magoya bayan APC da NNPP sun cika tituna domin tarbar Tinubu duk da ana ruwa, yayin da ya kai ziyarci iyalan mamacin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano – Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci gidan Alhaji Aminu Dantata, wanda ya rasu kwanan nan, domin mika ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin.

Ziyarar shugaban na zuwa ne bayan an kammala jana'izar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a Daura da ke jihar Katsina.

Shugaba Bola Tinubu ya gana da iyalan Alhaji Aminu Dantata domin yin masu ta'aziyya a Kano
Alhaji Aminu Dantata ya ziyarci Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa. Hoto: @DOlusegun
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Bola Ahmed Tinubu ya sauka a filin jirgin Malam Aminu Kano a yammacin Juma'a, 18 ga watan Yuli, 2025 domin ta'aziyyar Alhaji Dantata.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya isa Kano domin yin ta'aziyya, ba a ga Ganduje a wurin tarba ba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tunibu ya fadi halayen Dantata

Rahoto ya nuna cewa a ziyarar da ya kai Kano, Tinubu ya bayyana marigayi Dantata a matsayin fitaccen mai taimakon jama'a.

Ya ce daga cikin muhimman abubuwan da za a tuna marigayin da shi shi ne ciyar da talakawa fisabilillahi, nuna tausayi da kuma jin kai a gare su.

Ya kara da cewa dole ya yi takakkiya zuwa Kano, domin ya jajanta wa iyalan marigayin, gwamnatin Abba Kabir Yusuf da kuma al'ummar Kano baki daya.

Tinubu ya bayyana kusancinsa da Dantata

Ya kara da cewa Dantata mutum ne mai gaskiya, aminci da kuma taimako ga al’umma, wanda ya sadaukar da kansa wajen inganta rayuwar jama’a a ko’ina cikin duniya.

Tinubu ya bayyana hakan ne a gidan Dantata da ke unguwar Koki a Kano, a ranar Juma’a, yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayin.

Shugaban ya tuna cewa tun lokacin da yake yakin neman zaɓe, ya zo wa marigayin neman addu’a don samun nasara.

Kara karanta wannan

UNIMAID: An faɗi babban dalilin da ya sa Tinubu ya sauya sunan jami'a saboda Buhari

Jaridar The Guardian ta rahoto Tinubu yana cewa:

"Na zo nan lokacin yakin neman zaɓe domin neman addu’a, kuma ya yi mani. Wannan ziyarar ta’aziyya na Kano, ta ƙashin kaina ce, domin na nuna jimami ga iyalan marigayin da daukacin al’ummar Kano bisa wannan babban rashi.
Shugaba Bola Tinubu ya dura Kano domin yin ta'aziyyar Alhaji Aminu Alhassan Dantata
Gwamnan Kano, Abba Yusuf ya tarbi Shugaba Bola Tinubu a filin jirgi lokacin da ya dura kano don ta'aziyyar Dantata. Hoto: @DOlusegun
Source: Twitter

Kano: Magoya baya sun tarbi Tunibu

Dubbunan magoya bayan jam’iyyar APC da ta NNPP sun fito kwansu da kwarkwata domin tarbar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a jihar Kano.

Tinubu ya sauka Kano a filin jirgin saman Malam Aminu Kano (MAKIA) da yammacin ranar Juma’a, inda fitattun jiga-jigan jam’iyyun APC da NNPP suka tarbe shi, ciki har da Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Sauran sun hada da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I. Jibrin, Nasiru Gawuna, wanda ya tsaya takarar gwamna a ƙarƙashin APC a zaɓen 2019, da sauran manyan 'yan siyasa.

Daga filin jirgin saman MAKIA, jerin motocin Shugaba Tinubu suka wuce unguwar Koki da ke tsakiyar birnin Kano, inda gidan iyalan marigayi attajiri Aminu Alhassan Dantata ke.

Kara karanta wannan

Bayan Buhari, Bola Tinubu zai je jihar Kano ta'aziyyar Aminu Dantata

Ko da yake ruwan sama ya sauka sosai a lokacin, hakan bai hana dubunnan magoya bayan APC da NNPP cika titunan birnin Kano ba, suna nuna farin ciki da godiya bisa ziyarar ta’aziyyar da Tinubu ya kawo.

Waiwaye: Tinubu ya gana da Dantata a Villa

A baya, Legit Hausa ta rahoto cewa, hamshakin ɗan kasuwan Kano, Alhaji Aminu Dantata, ya kai ziyara fadar shugaban kasa a Abuja, inda ya gana da Shugaba Bola Tinubu.

Taron nasu ya gudana ne a ranar 22 ga Mayun 2024, kuma shi ne karo na farko da shugaban kasar ya gana da dattijon tun bayan rantsar da shi a ranar 29 ga Mayu, 2023.

Alhaji Dantata, wanda shi ne kawu ga attajirin nahiyar Afrika, Aliko Dangote, ya halarci fadar shugaban kasar domin tattaunawa da jinjina ga gwamnatin Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng