Za a Sheka Ruwa da Tsawa na Kwana 3 a Abuja, Kano da Jihohin Arewa 18 daga Juma'a
- Hukumar NiMet ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama mai yawa da tsawa a Arewacin Najeriya daga Juma’a zuwa Lahadi
- Jihohin da abin zai shafa sun haɗa da Borno, Gombe, Bauchi, Yobe da Kaduna, inda ruwan zai iya yin karfi a ranar Juma’a da Asabar
- A ranar Lahadi kuwa, ana sa ran ruwan sama mai ƙarfi da tsawa a sassan Kebbi, Adamawa, Neja, Kogi, Kwara da Abuja a safiya da yamma
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar kula da hasashen yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama mai karfi hade da tsawa daga Juma'a zuwa Lahadi.
Hasashen yanayin na NiMet wanda aka fitar a ranar Alhamis a Abuja, ya nuna cewa za a yi tsawa mai yawa hade da ruwa mai karfi a jihohin Arewa.

Kara karanta wannan
'Ku shirya': Yobe, Kano da jihohi 9 za su fuskanci ambaliyar ruwa daga ranar Lahadi

Source: Getty Images
Hasashen yanayi na ranar Juma'a
Hukumar ta yi hasashen ruwan sama mai matsakaicin karfi zuwa mai karfi a safiyar Juma'a a sassan jihohin Borno, Yobe, Kaduna, Bauchi da Gombe a cewar rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NiMet ta yi hasashen tsawa tare da ruwan sama mai matsakaicin karfi a lokacin La'asar ko Magriba a sassan jihohin Adamawa, Yobe, Sokoto, Zamfara, Bauchi, Borno, Gombe, Jigawa, Kaduna da Taraba.
A cewar NiMet, ana sa ran samun hadari da hudar rana a yankin Arewa ta tsakiya a safiyar Juma'a, sannan a samu ruwan sama a Plateau da Nasarawa.
Hukumar ta yi hasashen ruwan sama kaɗan zai sauka a sassan Plateau, Babban Birnin Tarayya (FCT), Nasarawa da Benue a yammacin ranar.
Hasashen yanayi na ranar Asabar
Sanarwar NiMet ta ci gaba da cewa:
"Ana sa ran samun hadari amma da hudar rana a duk tsawon safiyar a ranar Asabar.
"Ana sa ran tsawa tare da ruwan sama mai karfi a tsakanin La'asar zuwa dare a sassan jihohin Adamawa, Gombe, Jigawa, Kano, Katsina, Kebbi, Yobe, Taraba, Kaduna da Bauchi.
"Ga yankin arewa ta tsakiya, ana sa ran ruwan sama kaɗan a safiyar ranar a sassan Babban Birnin Tarayya, Plateau da Benue.
"A yammaci zuwa dare kuwa, ana sa ran ruwan sama kaɗan a sassan Plateau, Benue, Kogi, Neja, Kwara, Nasarawa da Babban Birnin Tarayya."

Source: Original
Hasashen yanayi a ranar Lahadi
NiMet ta yi hasashen cewa za a samu rana hade da hadari a ranar Lahadi a yankin Arewa.
Hukumar ta yi hasashen tsawa a sassan jihohin Adamawa, Taraba, Kaduna da Kebbi a safiyar ranar.
"Ana sa ran tsawa tare da ruwan sama a yankin daga yammaci zuwa dare.
"A Arewa ta tsakiya, za a samu ruwan sama a safiyar Lahadi a sassan Nasarawa, Neja, Babban Birnin Tarayya, Kogi, Benue, Kwara da Neja.
"Ana sa ran matsakaicin ruwan sama zuwa mai karfi a sassan Babban Birnin Tarayya, Nasarawa, Plateau, Neja, Kogi, Kwara da Benue daga yamma zuwa dare"
- Inji hukumar NiMet.
Jihohi 11 za su iya fuskantar ambaliya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ma’aikatar muhalli ta tarayya ta bayyana jihohi 11 da ke fuskantar barazanar ambaliya tsakanin 16 da 20 ga Yulin 2025.
Jihohin da abin ya shafa sun haɗa da Adamawa, Borno, Bauchi, Katsina, Kano, Plateau da wasu jihohi shida, kamar yadda sanarwar ta nuna.
Wannan hasashe na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnati ta kaddamar da shirin inshorar ambaliya don rage hasara da kare rayuka da dukiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

