Shugaba Tinubu Ya Isa Kano domin Yin Ta'aziyya, Ba a Ga Ganduje a Wurin Tarba ba

Shugaba Tinubu Ya Isa Kano domin Yin Ta'aziyya, Ba a Ga Ganduje a Wurin Tarba ba

  • Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya sauka a jihar Kano a wata ziyarar ta'aziyya bisa rasuwar fitaccen ɗan kasuwar nan mai taimako, Aminu Ɗantata
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf, mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin da wasu kusoshin gwamnatin Kano ne suka tarbi Tinubu yau Juma'a
  • Ɗantata ya rasu ne a lokacin Tinubu ya yi tafiya, amma duk da haka ya tura tawaga zuwa wurin jana'izar marigayin wanda aka yi a ƙasar Saudiyya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya isa Jihar Kano domin yin ta’aziyya ga iyalan marigayi dattijo kuma fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Aminu Dantata.

Jirgin shugaban ƙasa ya sauka a Filin Jirgin Sama na Aminu Kano da misalin ƙarfe 3:30 na yammacin yau Juma'a, 18 ga watan Yuli, 2025.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a Kano
Jirgin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya sauka a Kano Hoto: @NTANetwork
Source: Facebook

Gwamna Abba da Barau sun tarbi Bola Tinubu

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu zai halarci taron addu'a da Allah Ya karɓi rayuwar Mai Martaba Sarki

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ne suka tarbe shi tare da wasu manyan jami’an gwamnati, NTA News ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, na cikin tawagar jami’an gwamnati da suka raka Shugaba Tinubu zuwa Kano da ke Arewa maso Yamma.

Abubuwan da Tinubu zai yi a Kano

A yayin wannan ziyarar, ana sa ran Shugaban Ƙasa zai ziyarci iyalan Dantata domin miƙa ta’aziyyarsa.

Sannan kuma Shugaba Tinubu zai jajanta wa al’ummar Kano da gwamnatin jihar bisa rasuwar wannan babban ɗan kasuwa wanda ya kai shekaru fiye da 90.

Alhaji Aminu Dantata, mashahurin ɗan kasuwa kuma attajiri mai taimakon al’umma, ya rasu ne a ranar 28 ga Yuni, 2025, a birnin Abu Dhabi da ke Ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

Me ya hana Bola Tinubu zuwa ta'aziyya tun farko?

A lokacin rasuwar, Shugaba Tinubu ya yi tafiya zuwa ƙasashen waje ne, amma ya tura wata tawaga ƙarƙashin jagorancin Ministan Tsaro, Mohammed Badaru

Tawagar ta samu damar zuwa ƙasar Saudiyya domin halartar jana’izar marigayin a matsayin girmamawa gare shi da gudunmawar da ya bayar ga ƙasa.

Kara karanta wannan

"Ina kewarsa," Tinubu ya faɗi alaƙarsa da Ɗantata yayin ta'aziyya a Kano

Marigayi Alhaji Aminu Ɗantata.
Shugaba Tinubu ya kai ziyara Kano domin ta'aziyya ga iyalan Ɗantata Hoto: Bashir Ahmad
Source: Facebook

A ɗazu ne fadar shugaban ƙasa ta sanar da shirin Shugaba Tinubu na zuwa Kano a yau Juma'a, domin yi wa iyalan Ɗantata ta'aziyya da kansa, inji rahoton The Cable.

Sanarwar ta fito ne daga hannun mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, wanda ya wallafa a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter a baya.

Tinubu ya gana da Gwamna Eno a Villa

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karɓi baƙuncin shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio da gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno a fadarsa da ke Abuja.

Tawagar mai girma gwamnan ta ƙunshi wasu manyan ‘yan siyasa biyu daga jihar Akwa Ibom, inda suka gana da shugaban ƙasa domin tattauna batutuwa masu muhimmanci.

Duk da ba a bayyana ainihin abin da suka tattauna ba, amma majiyoyin sun ce ganawar ta maida hankali kan batutuwan da suka shafi ƙasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262