An Fara Fito da Bayanai kan 'Cabal', Gambari Ya Fallasa Yadda aka Mamaye Gwamnatin Buhari
- Tsohon shugaban ma'aikatan gwamnati tarayya, Farfesa Ibrahim Gambari ya ce tabbas akwai 'cabal' a lokacin Muhammadu Buhari
- Ya ce a lokacin, wadannan mutane na zagaye wa domin miƙa wasu takardu ga shugaban na tare da an bi tsarin da ya dace ba
- Gambari ya ce Buhari na da tausayin hadimansa, don haka yana jinkiri wajen sauke su daga mukamansu duk da matsin lamba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, ya yi magana kan zargin cewa wasu sun juya akalar gwamnatin Muhammadu Buhari.
Ya fallasa yadda wadanda ake zargin ke yin gaban kansu, suna mika takardun wasu bukatun ga tsohon shugaban kasa, Buhari ba tare da ya bi ta ofis dinsa ka.

Source: Twitter
A hira da ya yi da Channels TV, Farfesa Gambari ya ce waɗannan mutane na fakon shugaban kasar, sai su lallaba da takardun a lokacin da suka fuskanci dacewar haka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda 'cabal' su ka mamaye gwamnatin Buhari
Jaridar Punch ta wallafa cewa Farfesa Gambari ya ce waɗannan gungun mutane da aka yi wa lakabi da 'cabal' sun bijire wa umarnin Muhammadu Buhari.
A kalamansa:
“Suna sanin lokacin da yake da rauni, kuma suna sanin lokacin da za su shige masa da takardu, domin sun saba da shi a wuraren da ba na ofis ba.”
“Lokacin da na shiga ofis, Buhari ya ce dole ne dukkanin takardu su rika bi ta hannun shugaban ma’aikata kafin su iso gare shi."
“Ko mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, a matsayinsa, ya kan rika mika wa ofishi na takardunsa. Haka wasu ministoci ma."
"Amma duk da haka wasu mutane na samun hanyar kai masa takardunsu kai tsaye. Sun san inda zai fi sauki su shige masa. Shi kuma bai hana su ba, amma fa takardun sukan dawo hannuna daga baya.”
'Buhari na tausayin hadiminsa,' Gwamnati
Yayin da yake tunawa da rayuwarsa tare da marigayi shugaba Buhari wanda ya rasu a ranar 13 ga Yuli, 2025, Gambari ya ce:
“Buhari na son hadimansa kamar yadda yake son ’yan Najeriya. Wannan ne ya sa yake da jinkiri sosai wajen sauke wasu daga mukamansu, duk da kiraye-kirayen da ake yi masa.”
Gambari ya tabbatar da cewa koda kuwa akwai wasu mutane masu karfi da ke shafar shawarwarin shugaban kasa, ba su ketara iyakokinsu ba.

Source: Facebook
Ya ce:
“Ana cewa akwai masu juya gwamnati, eh akwai. Kowace gwamnati tana da nata. A lokacin Obasanjo ma akwai irin su Aboyade da wasu rukunin mutane ne. Hakan dai na cikin tsarin ofishin shugaban ƙasa.”
Yaran Buhari sun fara kewar ubansu
A baya, kun ji cewa har yanzu ana ci gaba da jimamin rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a Landan bayan ya sha fama da jinya.
Daga sassa daban-daban na ƙasar, mutane na ci gaba da bayyana alhini da ta’aziyya, ciki har da masu cewa sun yafe duk wani hakkinsu da ya rataya a wuyansa.
Aisha Hanan Buhari da Hadiza Muhammadu Buhari sun bayyana godiyarsu ga jama’a da suka nuna karamci da yafiya ga mahaifinsu tare da addu'a gare su.
Asali: Legit.ng


