Ni ne 'cabal', inji Isa Funtua

Ni ne 'cabal', inji Isa Funtua

Isa Funtua, daya daga na hannun daman Shugaba Muhammadu Buhari, ya ce baya cikin wadanda ake kira 'cabal' wato miyagu sai dai shine 'cabal' din da kansa.

Funtua, wanda dan asalin jihar Katsina ne kamar shugaban kasa yana daya daga cikin wadanda masu sukan gwamnatin Buhari ke kira a matsayin 'cabal' kamar yadda The Cable ta ruwaito.

A lokuta da dama, Aisha, matar shugaban kasa ta ce fadin cewa wasu na kusa da shugaban kasa sun kwace gwamnati daga hannunsa.

A cikin Disamban 2019, matar shugaban kasar ta zargi mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu da yi wa wasu daban biyaya a maimakon mijinta da ya yi rantsuwar yi wa 'yan Najeriya aiki a ranar 29 ga watan Mayun 2015 da 2019.

A jawabin da ya yi a shirin The Morning Show da aka nuna a Arise Television a ranar Asabar, Funtua ya ce cin fuska ne a ce wasu mutane ke tafiyar da gwamnati a maimakon Shugaba Muhammadu Buhari.

Funtua ya zargi mutane da amfani da kalmar cabal da mugun nufi inda ya ce shugaban kasa yana da ikon ya jawo mutanen da ya amince da su kusa da shi.

DUBA WANNAN: An kori wata musulma daga wurin aiki saboda ta saka hijabi

Ya ce, "Ba na cikin 'yan cabal, Ni ne cabal din."

Mene ne cabal? A takaici ina tunanin kalmar na nufin aminai, mutanen da mutum ya amince da su. Mutanen da ka yi imanin ba za su cuce ka ba kuma za su aikata abubuwa da za su amfani kasa.

"Yan Najeriya na amfani da cabal da mugun nufi kuma wannan bane ainihin ma'anarsa. Ka dauki kamus ka duba ma'anar cabal?

Da aka tambaye shi kan zargin da matar shugaban kasa ta yi na cewa akwai cabal, ya ce: "Ka da Allah ku kyalle ni, na roke ku."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel