Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Gwamnan da Ya Sauya Sheƙa zuwa APC, An Samu Bayani
- Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya gana da shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno
- Duk da ba a bayyana ainihin abin da suka tattauna ba, amma majiyoyin sun ce ganawar ta maida hankali kan batutuwan da suka shafi ƙasa
- Wannan dai na zuwa ne ƙasa da watanni biyu bayan Gwamna Eno ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC mai mulkin ƙasar nan
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya karɓi baƙuncin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio da Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Umo Eno.
Shugaban ƙasar ya gana da waɗannan manyan jiga-jigai a fadarsa da ke babbban birnin tarayya Abuja yau, 18 ga watan Yuli, 2025.

Source: Twitter
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ne ya tabbatar da hakan a wata gajeruwar sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Onanuga ya ce:
"Gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno, da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, sun kai ziyara ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Juma’a. Gwamna Eno shi ne jagoran APC a jiharsa."
Gwamna da tawagarsa sun gana da Tinubu
Wannan ganawa na cikin jerin shawarwari da Shugaba Tinubu ke yi da shugabanni daga jihohin ƙasar domin haɓaka haɗin kai da cigaba a matakin ƙasa da jihohi.
Gwamna Umo Eno, wanda shi ne jagoran jam’iyyar APC a jiharsa ta Akwa Ibom, ya samu rakiyar Sanata Akpabio, tsohon gwamnan jihar kuma shugaban majalisar dattawa na yanzu.
Haka zalika tawagar gwamnan ta ƙunshi wasu manyan ‘yan siyasa biyu daga jihar Akwa Ibom, inda suka gana da shugaban ƙasa domin tattauna batutuwa masu muhimmanci.
Gwamna Eno ya sauya sheƙa zuwa APC
Wannan ziyara dai na zuwa ne bayan Gwamna Eno ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan
UNIMAID: An faɗi babban dalilin da ya sa Tinubu ya sauya sunan jami'a saboda Buhari
Gwamna Eno ya sanar da haka ne a wani taro na musamnan da aka shirya a fadar gwamnatinsa da ke Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom ranar 6 ga watan Yuni, 2025.
Umo Eno ya bayyana cewa ya yanke hukuncin sauya sheƙa ne bayan watanni uku na shawara da tattaunawa da shugabanni da masu ruwa da tsaki a fadin jihar.

Source: Twitter
Me shugabannin suka tattauna a Aso Villa?
Makonni shida cif bayan haka, Gwamna Eno ya kawo wa Bola Tinubu ziyara a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja yau Juma'a.
Duk da babu cikakken bayani kan abin da suka tattauna, amma majiyoyi daga fadar sun nuna cewa ganawar ta fi karkata kan batutuwan da suka shafi haɓaka dangantaka tsakanin gwamnatin tarayya da ta jihar Akwa Ibom.
Haka zalika sun ce Tinubu, Eno, Akpabio da sauran jiga-jigan da suka halarci zaman sun tattauna kan yadda za a warware wasu batutuwan da suka shafi ci gaban ƙasa baki ɗaya.
Dalilin gwamnan Akwa Ibom na shiga APC
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Umo Eno ya ce ya yanke shawarar shiga APC ne saboda nasarorin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Ya ce Bola Tinubu ya samu nasarori a tarihin siyasarsa musamman lokacin da yake matsayin gwamnan jihar Legas daga 1999 zuwa 2007.
Ya kara da cewa Shugaban kasa, Tinubu ya nuna jarumta wajen tinkarar matsalolin tattalin arzikin kasa tare da daukar matakai masu wuya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

