'Shehu Dahiru Bauchi bai Yarda Inyass na Bayyana a Jikin Bango ko Sama ba,'
- Sayyid Ibrahim ya ce Sheikh Dahiru Bauchi bai yarda da masu cewa sun ga Shehu Inyass a bango ko bishiya ba
- Ya bayyana cewa hakan ƙarya ce da wasu ke amfani da ita domin yaudarar mutane da cin moriyar jahilci
- Ibrahim ya yi karin haske kan alaƙar su da Muhammadu Sanusi II da kuma cigaban Darikar Tijjaniyya a Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Turkiyya - Sayyid Ibrahim, ɗan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya bayyana cewa mahaifinsa bai yada da akidar da ke cewa ana ganin Shehu Ibrahim Inyass a bango, bishiya ko sama ba.
Malamin ya ce irin wannan magana yaudara ce da wasu ke amfani da ita don cutar da mutane, kuma ba gaskiya ba ce a addini.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanan da Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi ya yi ne a bidiyo da TRT ta wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ibrahim Dahiru Usman Bauchi ya bayyana hakan ne a wata hirar yayin wata ziyara da ya kai ƙasar Turkiyya a makon nan.
Maganar bayyanar Inyass a bango
A cikin hirar, Sayyid Ibrahim ya ce maganar bayyanar Inysa ta sabawa tunanin darikar Tijjaniyya kuma hakan bai dace ba sam sam.
'Dan gidan Shehi ya bayyana cewa wata dabara ce kawai wasu ke amfani da ita domin neman kudi wajen wadanda ba su da ilimi.
Ibrahim ya kuma tabbatar da cewa maganar bayyanar Inyass a bango ba ta da alaka da akidar Shehu Dahiru Bauchi.
Sanusi II Khalifan Tijjaniyya ne?
A kan batun shugabancin Darikar Tijjaniyya a Najeriya, Ibrahim ya bayyana cewa Darika tana da tsarin shugabanci na ladabi da bin umarni kamar gidan soja.
Ya ce suna da kyakkyawar alaƙa da Sarki Muhammadu Sanusi II, amma ba za a ce shi ne Khalifan Tijjaniyya a Najeriya ba.
“Na ce masa kai shugaba ne kuma ana buƙatarka, amma kai ba Khalifa ba ne,”
- Inji shi.
Shirin taron Tijjaniyya na duniya
Ibrahim Dahiru Bauchi ya bayyana cewa yana ƙasar Turkiyya ne saboda wata ziyara da aka daɗe ana nema, sama da shekara uku.
Ya ce ana shirin gudanar da babban taron Darikar Tijjaniyya na duniya wanda za a iya yi a Najeriya ko Senegal a ƙarshen wannan shekarar.
Tasirin Tijjaniya a Najeriya da duniya
Sayyid Ibrahim ya bayyana cewa Darikar Tijjaniyya tana da mabiya fiye da miliyan 400 a duniya, ciki har da makarantu fiye da 600 a Najeriya.
A cewarsa, makarantun Tijjaniyya na horar da yara ne wajen haddace Alƙur’ani cikin shekaru huɗu zuwa shida, kuma ba a barin malamai ko dalibai suna bara a tituna.

Source: Twitter
Ya bukaci a maida hankali wajen haɗa kai da kawo cigaba a Arewacin Najeriya maimakon ɓata lokaci a kan suka da rigingimu marasa amfani.
Ana gina makarantar Dahiru Bauchi
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya fara aikin makarantar Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Rahotanni sun bayyana cewa za a yi makarantar ne domin ba dalibai daga yankunan jihar damar samun karatu mai inganci.
Legit Hausa ta rahoto cewa Sanata Bala Mohammed ya gina makarantar da sunan Shehi saboda gudumawar da ya bayar a jihar.
Asali: Legit.ng


