Toh fa! Shehu Dahiru Bauchi ya tabbatar tare da gaskata bayyanar Inyass a fitilar kan titin ABuja
Dangane da labarin da ake yadawa na cewa wai Inyass ya bayyana a yayin taron Maulidinsa da mabiya darikar Tijjaniyya suka gudanar a babban birnin tarayya Abuja, shahrarren Malamin Tijjaniyya, Dahiru Bauchi ya tabbatar da lamarin.
Jaridar Rariya ta ruwaito Dahiru Bauchi na cewa bayyana waliyyai a wurare daban daban, kamar yadda Inyass ya bayyana maulidin Abuja wata karama ce da Allah ke yi ma bayinsa waliyyai.
KU KARANTA: Yawanci matasan Najeriya basu son karatu, sun fi kaunar zaman kashe wando – Buhari daga Landan
Majiyar Legit.ng ta ruwaito shehin Malamin ya cigaba da cewa “Ai wannan babu wani abin mamaki game da shi, Allah yayi haka ne don ya nuna ma mutane cewa karamar Waliyyar gaskiya ce. Don haka yana iya bayyana a ko ina.”
Dahiru Bauchi bai tsaya ba har sai da yace: “Wasu jama’a sun sha ganin Inyass a dakunansu, wani lokaci ma yak an bayyana haka nan kawai, wannan ba wani abin mamaki bane game da karamar Shehu, tsabar karama ce kawai.”
Daga karshe Shehin Malamin ya karkare da cewa waliyyai na iya yin wasu abubuwan da sauran jama’an gama gari ba zasu ko kwatanta yin sa ba.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng