'Zai Yi Wahala Obi Ya Yi Shugaban Kasa, Hadimin Buhari ya yi Martani ga Obidients
- Hoton tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi da na hadimin tsohon shugaba, Muhammadu Buhari ya tayar da kura
- Bashir Ahmad ne dai ya wallafa hoton bayan ta'aziyyar rasuwar tsohon shugaban kasa da ya kai Daura, jihar Katsina
- Lamarin bai yi wa wasu dadi ba, musamman magoya bayan Peter Obi da su ka yi wa Bashir dirar mikiya kan zargin an yi maganar siyasa
Jihar Katsina – Bashir Ahmad, tsohon mai taimaka wa marigayi shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kare kansa daga sukar magoya bayan Peter Obi a shafin sada zumunta.
Ya ce ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya nemi goyon bayansa a lokacin wata ganawa da suka yi a Daura, jihar Katsina.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jama'a sun soki Bashir Ahmad saboda hoton da ya ɗora na shi da Obi a lokacin da ɗan siyasar ya kai ziyarar ta’aziyya.

Kara karanta wannan
Hoton yadda Aisha Buhari ta rungume tutar da aka lulluɓo gawar mijinta ya ja hankali
Bashir Ahmad ya kare kansa
PM news ta wallafa cewa Obi ya ziyarci Daura ne domin jajanta wa iyalan marigayi Muhammadu Buhari, kwana guda bayan jana’izarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A nan ne suka hadu, har Bashir Ahmad ya wallafa hotonsu da taken "Ganawa ta da @PeterObi a Daura", lamarin da wasu ke ganin kamar akwai lauje cikin nadi.
Amma a bayaninsa, Bashir ya ce:
“Lokacin da na isa gidan Baba da safe, na iske manyan baki da dama a wajen. Na fara gaisawa da Malam Mamman Daura, sai na wuce wajen Atiku Abubakar, wanda ke zaune a kusa da shi. Sannan na gaida Malam Nasir El-Rufai da kuma Mista Peter Obi, wanda ke zaune kusa da su."
Ya ci gaba da cewa:
"Mista Obi ya ambaci wani abu da na wallafa a Twitter. Na murmusa kawai na ci gaba da gaisawa da sauran baki. Daga baya, sai @YunusaTanko ya sake nuna ni, domin bai san cewa na riga na gaisa da shugabansa ba. Obi ya sake jajanta rasuwar Baba kuma ya ce yana yabawa da irin biyayyata ga Baba koda bayan barinsa ofis.”
Yadda Obi ya nemi goyon bayan Bashir
Bashir Ahmad ya ce babu wata tattaunawa ta siyasa a tsakaninsu sai daga baya, kafin Obi ya tafi, inda suka tsaya dan gajeren lokaci.
Ya ce:
“A lokacin, Mista Obi cikin nishadi ya ce na zo na mara masa baya. Ya kuma bayyana yadda ya ga filayen noma masu faɗi a hanyar zuwa Daura."
Ya bayyana mamakinsa da yadda wasu daga cikin magoya bayan Peter Obi, da aka fi sani da “Obidients”, suka fara kai masa hari bayan wallafa hoton

Source: Twitter
Ya ce:
.“Gaskiya, na zata harin zai fito daga ‘yan jam’iyyata, amma abin mamaki shi ne, na fi samun fahimta daga cikin gida. Sun gane ba siyasa aka yi ba, illa ta’aziyya ce kawai.
Bashir ya ce, irin halayen masu goyon bayan Obi na kora mutane da cin zarafi zai iya hana Obi kafa goyon bayan da za ta iya kai shi ga kujerar shugaban ƙasa.
Buhari: Bashir Ahmad ya gode wa Atiku
A baya, kun samu labarin cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya nuna girmamawa ga marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Atiku, wanda ke da wata tafiya ta kasuwanci a ƙasashen waje, ya yanke hukuncin dakatar da ita domin ya samu damar halartar jana’izar Muhammadu Buhari.
Lamarin ya dadaɗawa makusantan Buhari kamar Bashir Ahmad, wanda ya gode wa Atiku Abubakar kan yadda ya ɗauki tsohon shugaban kasa da daraja.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

