UNIMAID: Tinubu Ya Karrama Marigayi, Ya Sauya Sunan Jami'ar Tarayya zuwa Buhari

UNIMAID: Tinubu Ya Karrama Marigayi, Ya Sauya Sunan Jami'ar Tarayya zuwa Buhari

  • Shugaba Bola Tinubu ya sanar da sauya sunan Jami’ar Maiduguri zuwa 'Muhammadu Buhari University', a matsayin girmamawa
  • Tinubu ya ce Buhari mutum ne mai gaskiya da rikon amana, wanda bai yarda da son rai ko tafiye-tafiyen siyasa marasa tushe ba
  • Shugaban ya bayyana cewa Buhari ya kafa tsari na gaskiya da rikon gaskiya da zai ci gaba da zama madubi ga shugabannin gaba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauya sunan jami'ar Maiduguri domin karrama Muhammadu Buhari.

Tinubu a ranar Alhamis ya bayyana cewa za a sauya sunan Jami’ar Maiduguri domin girmama marigayi Muhammadu Buhari.

Tinubu ya karrama marigayi Muhammadu Buhari
Tinubu ya sauya sunan jami'ar Maiduguri zuwa suna Buhari. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Shugaba Tinubu ya kwarara yabo ga Buhari

Hakan na cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga ya tabbatar a yau Alhamis 17 ga watan Yulin 2025 a shafin X.

Kara karanta wannan

Ana ci gaba da bayyana ayyukan alheran Buhari, Malami faɗI abin da ya sani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cikin sanarwar, ya ce za a ci gaba da kiran jami'ar Maiduguri da 'Muhammadu Buhari University', Maiduguri.

A yayin da yake jagorantar zaman, Shugaba Tinubu ya gabatar da jawabi mai taba zuciya, inda ya yabawa rayuwar Buhari da ya ce cike take da ladabi da kishin kasa.

Darasin da Tinubu ya koya daga Buhari

Tinubu ya ce rayuwar Buhari cike take da kamun kai, gujewa amfani da iko, da tsayawa kan gaskiya komai wahalar lamarin.

A cewarsa:

"Buhari ya tsaya tsayin daka, bai rinjayu da son zuciya ba, bai dogara da yabo ba, kuma bai ji tsoron yin abin da ya dace ba.”
Tinubu ya karrama tsohon shugaban kasa, Buhari
Tinubu ya sauya sunan jami'a guda saboda Buhari. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Tinubu ya tuna alherin Buhari gare shi

Tinubu ya bayyana cewa Buhari ya kafa daidaito a mulki da ya samo asali daga gaskiya, adalci da jarumta.

Yayin da ya waiwayi hadin gwiwarsu a siyasance, Tinubu ya tuna yadda hadinsu da wasu daga kowane yanki ya haifar da sauyin mulki cikin lumana a 2015.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya fadi babbar girmamawar da ta rage Tinubu ya yi wa Buhari

Ya ce shugabancin Buhari a lokacin ya kasance mai kunya da kima, inda ya rike nauyin mulki ba tare da gunaguni ba.

Ko da yake kowane tarihi yana jawo bincike, Tinubu ya jaddada cewa rikon gaskiyar Buhari da da’a su ne abin koyi ga shugabanni masu zuwa.

Ya ce Buhari ya nuna kishin kasa da ayyukansa fiye da maganganu, kuma hakan ba ya neman yabo.

Tinubu ya sauya sunan jami'a saboda Buhari

Zaman na musamman da majalisar zartarwa ta gudanar ya kare da addu’o’i da jimamin mutuwar Buhari.

Tinubu ya bayyana sauya sunan Jami’ar Maiduguri a matsayin hanyar tunawa da Buhari a yanki da ya sha wahala a hannun ‘yan ta da kayar baya.

Zulum ya sauya sunan jami'a a Borno

Kun ji cewa gwmanan Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum ya amince da sauya sunan jami'ar jihar zuwa Jami'ar Kashim Ibrahim.

Zulum ya amince da hakan ne a taron majalisar zartarwa ta jiha (SEC) na farko a 2025 wanda ya gudanar a fadar gwamnatinsa.

Kwamishinan yaɗa labarai na Borno, Farfesa Usman Tar ya ce majalisar ta amince da sauya sunayen tituna da yi wa gidaje lambobi a birane.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.