'Yan Ta'adda Sun Yiwa Sojoji Tayin Cin Hancin N13.7m, Wani abu Ya Faru a Filato

'Yan Ta'adda Sun Yiwa Sojoji Tayin Cin Hancin N13.7m, Wani abu Ya Faru a Filato

  • Sojojin Operation Safe Haven sun ƙi karɓar cin hancin Naira miliyan 13.7 da wasu 'yan ta’adda suka ba su a hanyar Jos zuwa Sanga
  • An kama mutum biyu da ake zargi, an kwato makamai, harsasai, mota da kuɗi, kuma sojoji sun amsa kiran gaggawa tare da aiwatar da hare-hare a jihohi biyu
  • An kashe wasu ‘yan ta’adda, an kama 12, an ceto mutane uku da aka sace, an kuma kwato kayan aiki da haramtattun kwayoyi daga masu laifi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hedikwatar tsaro (DHQ) ta bayyana cewa sojojin Operation Safe Haven sun ƙi karɓar cin hanci na Naira miliyan 13.7 da ƴan ta'adda suka bayar a jihar Filato.

Daraktan yaɗa labaran hedikwatar tsaro, Manjo-Janar Markus Kangye, ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin wani taron manema labarai kan ayyukan sojoji a faɗin ƙasar.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Mamakon ruwan sama ya jawo ambaliya a gari, mutane 54 sun mutu

Hedikwatar tsaro ta ce dakarun soji sun ki karbar tayin N13.7m daga 'yan ta'adda
Mai magana da yawun hedikwatar tsaro (DHQ), Manjo-Janar Markus Kangye. Hoto: @DHQNigeria
Source: Twitter

Sojoji sun ki karbar cin hancin N13.7m

A cewarsa, sojojin sun amsa kiran gaggawa ne game da ayyukan ta'addanci lokacin da suka ci karo da waɗanda ake zargi, waɗanda suka yi yunƙurin ba su cin hanci, inji rahoton The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manjo-Janar Kangye ya ce:

"A ranar 9 ga Yulin 2025, jaruman sojojinmu sun tare wata mota da aka gani da ramukan harsashi a kan hanyar Jos zuwa Sanga.
"Waɗanda ake zargi sun yi yunƙurin rarrashin sojoji da kuɗi, amma suka ƙi. Sojoji sun kama mutane biyu da ake zargi, sun kwato makamai, harsasai, mota da kuma Naira 13,742,000.00 daga hannunsu.

Ya ce wadannan kudaden ne wadanda ake zargin suka yi yunkurin toshe bakin jami'an da su don su sake su, amma suka ki karba.

Sojoji sun gwabza fada da 'yan ta'adda

Hedikwatar tsaron ta jaddada cewa sojoji sun gudanar da ayyuka daga ranar 9 zuwa 16 ga Yuli 2025, inda sojojin Operation Safe Haven suka gudanar da hare-hare.

Kara karanta wannan

NiMet: Za a sha ruwa da tsawa a Kano, Yobe da jihohin Arewa 13 a ranar Lahadi

Hakazalika sojojin sun amsa kiran gaggawa game da ayyukan ta'addanci a yankunan ƙananan hukumomi da yawa a faɗin jihohin Plateau da Kaduna.

A yayin waɗannan ayyukan, sun yi arangama da kuma kashe wasu ƴan ta'adda, sun kama mutane 12 da ake zargi, kuma sun ceto mutane uku da aka sace.

"Daga 9 zuwa 16 ga Yulin 2025, sojojin Operation SAFE HAVEN sun gudanar da ayyukan kai hari kuma sun amsa kiran gaggawa kan ayyukan ƴan ta'adda a ƙananan hukumomin Bassa, Barkin Ladi, South Wase, Riyom da Jos East na Jihar Filato, da kuma ƙananan hukumomin Kaura da Sanga na Jihar Kaduna.

- Manjo-Janar Markus Kangye.

Hedikwatar tsaro ta yi bayani kan ayyukan sojoji daga 9 zuwa 16 ga Yulin 2025 a sassan Najeriya.
Hedikwatar tsaro (DHQ) ta ce sojoji sun kashe 'yan ta'adda, sun kama wasu, kuma sun ceto wadanda aka sace. Hoto: @DHQNigeria
Source: Twitter

Sojoji sun kwato kayayyaki daga 'yan ta'adda

Kakakin hedikwatar tsaron ya kara da cewa:

"Yayin da suke gudanar da waɗannan ayyukan, sun yi arangama da ƴan ta'adda kuma sun kashe wasu daga cikinsu, sun kama 12 kuma sun ceto mutane uku da aka sace. An kwato wasu makamai, harsasai, babura da motoci daga hannunsu.
"Hakazalika, sojojin Operation SAFE HAVEN yayin da suke sintiri na yau da kullum, sun kama masu laifi 7 a ƙananan hukumomin Barkin Ladi da Jos ta Kudu na jihar Filato da kuma ƙananan hukumomin Wamba da Sanga na jihohin Nasarawa da Kaduna.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun gwabza kazamin fada da ƴan bindiga a Nasarawa, an samu asarar rai

"Abubuwan da aka kwato daga gare su sun hada da makamai, harsasai da babura da kuma haramtattun kwayoyi."

Ya bayyana cewa bincike kan lamarin yana ci gaba da gudana, kuma dukkan abubuwan da aka kwato suna hannun sojoji.

Sojoji sun kashe hatsabiban 'yan bindiga 16

A wani labarin, mun ruwaito cewa, hedikwatar tsaro ta ce sojoji sun kashe shahararrun 'yan bindiga shida tare da wasu mayaƙa 10 a jihar Zamfara.

Cikin sunayen manyan da aka halaka akwai Auta, Abdul Jamilu, Salisu, Babayé, da ɗan Ado Alieru, kamar yadda sanarwar DHQ ta tabbatar.

Hedikwatar ta ce wannan samame na nuna jajircewar rundunar soji wajen murƙushe 'yan ta'adda da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com