Akpabio Ya Isa Daura don Ta'aziyyar Buhari, Ya Fadi Dabi'un Tsohon Shugaban
- Har yanzu shugabanni a matakai daban-daban na ci gaba da tururuwa zuwa jihar Katsina domin ta'aziyyar Muhammadu Buhari
- Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya jagoranci wakilan Majalisar Tarayya zuwa Daura domin ta su ta’aziyya
- Akpabio ya bayyana Buhari a matsayin gwarzon ƙasa da ya sadaukar da rayuwarsa ga Najeriya da koyar da kishin ƙasa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Katsina – Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya jagoranci tawagar ’yan majalisar tarayya zuwa garin Daura da ke jihar Katsina.
Tawagar ta kai ziyarar domin ta’aziyya ga Gwamna Dikko Umaru Radda, kan rasuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Source: Facebook
The Nation ta wallafa cewa a yayin jawabi a lokacin ziyarar, Akpabio ya bayyana marigayi Buhari a matsayin gwarzon ƙasa, mutum mai gaskiya da rikon amana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akpabio ya fara da bayyana tsohon shugaban da dattako a yadda ya yi wa Najeriya hidima a matsayin soja da kuma shugaban da aka zaba ta dimokuraɗiyya.
Buhari: Tawagar Akpabio ta isa Katsina
Channels TV ta ruwaito cewa Akpabio ya bayyana cewa sun sha wahala a yunkurin su na zuwa ranar da ta gabata, inda jirginsu bai samu sauka ba.
Hakan ya samo asali ne saboda rufewar filin jirgin sama, lamarin da ya tilasta masu koma wa Abuja bayan fiye da sa’a biyu suna zagaya wa.

Source: Twitter
Ya ce:
"Mun nace sai mun dawo yau, domin girmama mutumin da ya sadaukar da komai domin Najeriya."
Shugaban majalisar ya kara da cewa Buhari ya bar tarihi mai kyau na ladabi, kishi da rikon gaskiya da kuma amana.
Gwamna Radda ya bayyana kusancinsa da Buhari
A nasa bangaren, Gwamnan jihar Katsina, Umaru Dikko Radda ya nuna godiyarsa ga ziyarar, inda ya bayyana yadda ya sha kai ziyara wajen Buhari tun bayan ritayarsa daga mulki.
A kalamansa:
“Tun bayan saukarsa, ina ziyartar Baba duk bayan makonni biyu zuwa uku. A kullum yana tunatar da ni da in ji tsoron Allah, na yi mulki da adalci, kuma na ƙaunaci wannan ƙasa."
“Buhari mutum ne da idan ka duba daga nesa zaka ce ba shi da kusanci da jama’a, amma idan ka same sa a kusa, mai tausayi ne kuma abin koyi.
Rasuwarsa babban rashi ne ga Katsina, Najeriya, da dukkanninmu da muka ɗauke shi tamkar uba.”
Gwamnan, ya kara da addu'ar Allah Ya jikan Muhammadu Buhari tare da sanya shi a aljanna maɗaukakiya.
Mai ɗaukar hoton Buhari ya shiga jimami
A wani labarin, kun ji cewa Bayo Omoboriowo, tsohon mai ɗaukar hoto na musamman ga marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya faɗa jimami.
Ya bayyana yadda Muhammadu Buhari ya ba shi cikakkiyar dama da ‘yanci wajen aiwatar da aikinsa na tsawon shekaru takwas ba tare da katsalandan ba.
Omoboriowo ya bayyana yadda tsohon shugaban ya amince da shi gaba ɗaya tun daga farkon aikinsa a matsayin mai ɗaukar hoto na fadar shugaban ƙasar nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

