Shettima, Gwamnoni, Bala Lau, Jingir, Makari da Jiga Jigai Sun Dura Gidan Buhari
- An gudanar da addu’ar rana ta uku ga marigayi Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a gidan shi da ke Daura, Jihar Katsina
- Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima da wasu gwamnoni da ministoci na cikin wadanda suka halarci addu'ar
- Shugabannin JIBWIS daga sassa daban-daban na ƙasa sun kai ziyarar ta’aziyya tare da yaba wa da halayen marigayin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina – An gudanar da addu’ar uku ga marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a gidan shi da ke garin Daura a Jihar Katsina.
Taron addu’ar ya samu halartar manyan jami’an gwamnati ciki har da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da wasu gwamnoni, bisa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Source: Facebook
Hadimin mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya wallafa yadda aka gudanar da taron a shafin shi na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shettima ya jagoranci addu’a a Daura
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya isa Daura da safiyar Alhamis tare da jagorantar taron addu’ar da aka gudanar a gidan Buhari.
Tare da Shettima akwai tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Namadi Sambo, Gwamna Dikko Radda na Katsina, Gwamna Babagana Umara Zulum na Borno, da wasu ministocin tarayya.

Source: Twitter
Bayan isarsa, Shettima ya fara da jajanta wa 'yan uwan marigayin sannan suka shiga taron addu’a da sauran mahalarta domin roƙon Allah ya gafarta wa marigayi Buhari.
JIBWIS-Kaduna ta yabi Muhammadu Buhari
Shugaban ƙungiyar JIBWIS ta ƙasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya kai ziyarar ta’aziyya tare da tawagarsa zuwa gidan marigayin a Daura da safiyar Alhamis.
Sheikh Bala Lau ya bayyana cewa Buhari ya kasance aboki na musamman ga ƙungiyar, inda ya ce ya halarci tarukanta.
JIBWIS ta wallafa a Facebook cewa marigayin ya kasance mutum nagari, mai kishin ƙasa da ƙoƙari wajen ganin ya gyara Najeriya.

Kara karanta wannan
Shettima, Atiku, gwamnoni da jiga jigan da suka koma gidan Buhari awanni 24 bayan birne shi
Bala Lau ya kara da cewa Buhari ya halarci buɗe katafaren masallacin da ƙungiyar su ta gina a Abuja a lokacin da yake kan mulki.
Tawagar ta haɗa da manyan shugabannin ƙasa na ƙungiyar JIBWIS ciki har da Dr. Ibrahim Jalo Jalingo, Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe, da Mustapha Imam Sitti.
JIBWIS-Jos ta yi ta’aziyya ga iyalan Buhari
Shugaban malamai na ƙasa na Izalar Jos, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ya kai ziyarar ta’aziyya zuwa Daura tare da tawagar malamai.
Sheikh Jingir ya yi gaisuwa ga iyalan marigayi Buhari, gwamnati da al’ummar Najeriya baki ɗaya, bisa rashin wannan babban jigo na ƙasa.
A cikin tawagar da ta zo daga Jos akwai Sheikh Dalha Abubakar Hakimi, Al-Hafiz Bala Yusuf, da Hon. Muhammad Muh’d Abubakar da sauran jami’an ƙungiya.
Farfesa Makari ya rufe taron da addu’a
Babban limamin Masallacin Ƙasa da ke Abuja, Farfesa Ibrahim Makari, ya kasance daga cikin wadanda suka halarci taron.
Legit ta gano cewa Farfesa Ibrahim Makari ne ya rufe taron da addu’a bayan Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi jawabi.
Za a yi wa Buhari addu'a a Abuja

Kara karanta wannan
Ana tsakiyar jimamin rasuwar Buhari, an maka Shugaba Tinubu da wasu jiga jigai a kotu
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta shirya taro na musamman ga marigayi shugaba Muhammadu Buhari.
Fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa a yammacin yau Alhamis za a yi taron majalisar zartarwa domin girmama Buhari.
Baya ga haka, a gobe Juma'a za a yi addu'a ta musamman ga Buhari a masallacin kasa a Abuja, sai kuma a masa addu'a a coci ranar Lahadi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
