'Yadda Buhari Ya Yaƙi Bankin Duniya da IMF domin Kare Talakan Najeriya'
- Tsohon shugaban kungiyar kwadago, Ayuba Wabba, ya yi jimamin rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari
- Wabba ya bayyana rasuwar Buhari a matsayin babban rashi ga talakawa da ma'aikata saboda manufofinsa na jin kai
- Kwamred Wabba ya ce Buhari ya ki cire tallafin mai duk da matsin lamba daga IMF da Bankin Duniya saboda yan Najeriya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Tsohon shugaban kungiyar kwadago, NLC da ITUC, Ayuba Wabba, ya yi jimamin rasuwar Muhammadu Buhari.
Wabba ya ce rasuwar Buhari babban rashi ne ga ma’aikata da talakawan Najeriya baki daya.

Source: Twitter
Yadda ma'aikata suka amfana da Buhari
Vanguard ta ce Wabba ya bayyana rasuwar Buhari abin bakin ciki ne, musamman ga ma’aikatan da suka amfana da manufofinsa masu tausayi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wabba ya tuna lokacin da dattijon ya hau mulki a 2015, Buhari ya amince da tallafin dala biliyan 2.1 don biyan albashi da fansho.
Ya ce:
“Abin da aka shirya a matsayin duban lafiya a London ya rikide zuwa rasuwar shugaban da ya tsaya tsayin daka tare da talakawa.
“Ya damu matuka da halin da ma’aikata ke ciki. Ya tambayi gwamnoni yadda suke iya barci yayin da ma’aikata ke binsu bashi."

Source: Twitter
Tallafin Buhari da wasu jihohi suka cinye
A 2017, Buhari ya sake sakin bilyoyin Naira domin taimaka wa jihohi biyan albashi da fansho.
Ayuba Wabba ya jinjinawa Buhari kan tattaunawar mafi karancin albashi da ya yi a lokacin mulkinsa.
“Abin takaici, wasu gwamnoni sun karkatar da kudin, Buhari ya gabatar da adadin da ya fi N30,000 kafin gwamnoni su hana hakan."
- Cewar Wabba
Wabba ya ce babbar manufar Buhari da ta yi amfani ga talakawa ita ce kin cire tallafin man fetur duk da matsin lamba daga Hukumar IMF da wasu a waje.
Ya kara da cewa:
“Duk da matsin lamba daga IMF da Bankin Duniya, Buhari ya ki kara farashin mai domin kare rayuwar talakawa."
Ya ce tarihi ba zai auna shugabanni da jawabi ba, sai dai da tasirin da suka yi a rayuwar al’umma, musamman ma’aikata da talakawa.
Wabba ya roki Allah ya gafarta wa Buhari, ya sa ya huta ya kuma ba shi gidan aljanna firdausi madaukakiya.
“Buhari ya bambanta a inda ya fi muhimmanci, wajen taimaka wa ma’aikata, ‘yan fansho da matalauta.
"Ina mika ta’aziyya ga Aisha Buhari da danginsa baki daya"
- Ayuba Wabba
Jigon ADC ya ce babu kamar Buhari
Kun ji cewa jigo a ADC, Salihu Lukman ya yi magana kan irin ƙalubalen da jagororin haɗaka za su iya fuskanta kan zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Salihu Lukman ya bayyana cewa a cikin haɗaka babu mutum mai tasiri irin na tsohon shugaban ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari.
Tsohon jigo a APC ya buƙaci ƴan haɗakar da su zama masu ƙanƙan da kai tare da gina ɗabi'ar yin aiki tare idan suna son samun nasarar kafa gwamnati a Najeriya.
Asali: Legit.ng

