Kalaman Buhari 3 da har Yanzu Suke Tayar da Jijiyoyin Wuya duk da Allah Ya Masa Rasuwa

Kalaman Buhari 3 da har Yanzu Suke Tayar da Jijiyoyin Wuya duk da Allah Ya Masa Rasuwa

  • Duk da Allah ya yiwa Muhammadu Buhari rasuwa, ƴan Najeriya na ci gaba da bayyana ra'ayoyi mabanbanta kan wasu kalamai da ya faɗa a mulkinsa
  • Kwatanta ƴan kabilar Igbo da "digo cikin da'ira" da kuma wasu kalamansa game da rawar mata a al'umma na ci gaba da jawo ka-ce-na-ce a kasar nan
  • Har yanzu da ba ya raye, ƴan Najeriya na ci gaba da nuna ɓacin ransu kan halin da aka shiga lokacin da CBN ya sauya takardun N200, N500 da N1000

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Daura, Katsina - Bayan rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, mutane da dama a Najeriya na ci gaba da tunawa da wasu kalamansa a lokacin mulkinsa

Yayin da wasu ke yabon jagorancinsa, wasu kuma na tunawa da wasu abubuwa da manufofin da suka bar tarihi mai sarkakiya, waɗanda har yanzu suke jawo ra'ayoyi mabanbanta.

Kara karanta wannan

'Ya taɓa korarmu kan N15': Diyar Buhari game da tarbiyya da mahaifinsu ya ba su

Marigayi Tsohon Shugaba Muhammadu Buhari.
Buhaɗi ya rasu amma ya bar abubuwa da ƴan Najeriya za su ci gaba tunawa Hoto: @MBuhari
Source: Twitter

Channels tv ta tattaro cewa Buhari ya rasu ne ranar Lahadi, 13 ga watan Yuli, 2025 a wani asibiti a birnin Landan na ƙasar Burtaniya bayan fama da jinya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga wasu kalamai guda uku da Marigayi Shugaba Buhari ya faɗa a gwamnatinsa wanda har yanzu suke tayar da jijiyoyin wuya a tsakanin ‘yan Najeriya har bayan rasuwarsa:

1. Kiran 'yan Igbo “digo a cikin da'ira”

Ɗaya daga cikin kalaman Buhari da suka fi jawo cece-kuce shi ne lokacin da ya kwatanta kabilar Igbo da “digo a cikin da'ira” a yayin yakin neman zaɓen 2015.

Wasu ƴan Najeriya musamman ƴan kabilar Igbo sun ɗauki wannan kalma a matsayin nuna ƙyamar ƙabila.

Mutane da dama musamman daga kudu maso gabas sun ɗauki kalaman a matsayin cin mutunci da wulakanta su.

Wani masani a siyasa ya ce: “Irin waɗannan kalmomi na ƙara rura wutar ƙiyayya a ƙasar da ke da ƙabilu iri-iri kamar Najeriya.”

Kara karanta wannan

"Bai so": Buba Galadima ya fadi dalilin jawo Buhari cikin harkar siyasa

2. Kalaman da Buhari ya faɗa kan mata

Wani abu da ya jawo fushin jama’a shi ne lokacin da Buhari ya ce mata sun fi dacewa da "ɗakin girki, falo da ɗayan ɗaki,” yayin da ya kai ziyara ƙasar Jamus a 2016.

Wannan furuci ya janyo suka daga ko’ina a duniya, inda aka bayyana kalaman tsohon shugaban ƙasar a matsayin na nuna wariyar jinsi da raunana matsayin mata.

Wata mai rajin kare haƙƙin mata ta ce:

“Irin waɗannan kalamai na tauye darajar mata kuma suna wulaƙanta muhimmancin rawar da mata ke takawa a fannoni daban-daban na rayuwa.”
Tsohon shugaban kasa, Muhammasu Buhari.
Har yanzu yan Najeriya na tuna yadda Buhari ya dage sai an canza takardun Naira Hoto: Bashir Ahmad
Source: Twitter

3. Karancin takardun Naira

A lokacin mulkin Shugaba Buhari, Babban Bankin Najeriya ya fito da sabon tsarin sauya fasalin kuɗi da nufin rage cin hanci da aiwatar da tsarin mu'amala da kuɗi ta intanet.

Amma yadda aka aiwatar da shirin ya janyo matsanancin ƙarancin kuɗi a hannun jama'a. Sai dai Buhari ya dage cewa tsarin yana da amfani a tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Mutanen Daura sun fadi yadda Buhari ya rayu a tsakaninsu bayan sauka a mulki

’Yan Najeriya da dama sun shiga mawuyacin hali wajen samun tsabar kuɗi don gudanar da rayuwar yau da kullum.

Hakan ya haifar da suka da fushin ƴan Najeriya a sassa daban-daban, inda mutane ke cewa gwamnati ba ta ɗauko hanyar aiwatar da tsarin yadda ya dace ba.

Wasu muƙarraban Buhari sun ci amanarsa

A wani labarin, kun ji cewa tsohon ɗan Majalisar Wakilai ya yi ikirarin cewa wasu daga cikin muƙarraban Marigayi Muhammadu Buhari sun ci amanarsa.

Dachung Bagos ya ce cin amanar da suka yiwa Marigayi Buhari ne ya haddasa kara tabarbarewar cin hanci da rashawa a lokacin mulkinsa.

Bagos ya amince cewa Buhari ya shahara a matsayin mutum mai gaskiya, amma matsalolin tsaro da suka addabi ƙasar nan a mulkinsa babban abin damuwa ne.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262