Rasuwar Buhari Ta Sa Jigo a APC Ya Yi Nasiha Mai Ratsa Zuciya ga Shugabanni
- Farfesa Muhammad Kailani ya jawo hankalin shugabanni kan rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari
- Jigon na jam'iyyar APC ya shawarce su da su yi shugabanci na gaskiya domin su ma wata rana za su bar duniya
- Farfesan ya nuna cewa Buhari ya yi iya ƙoƙarinsa amma wasu tsirarun mutane ne suka karɓe ikon gwamnatinsa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Jigo a jam'iyyar APC, Farfesa Muhammad Kailani, ya ba shugabannin Najeriya shawara kan rasuwar Muhammadu Buhari.
Farfesa Muhammad Kailani ya tunatar da shugabannin Najeriya cewa wata rana su ma za su mutu kamar yadda shugaba Buhari ya rasu.

Source: Twitter
Muhammad Kailani wanda ya daɗe yana ɗaya daga cikin abokan siyasar Buhari, ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake zantawa da manema labarai a birnin Abuja, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jigon APC ya ba da shawara kan rasuwar Buhari
Ya ja kunnen shugabanni kan gazawa wajen samar da kyakkyawan shugabanci, yana mai cewa lallai wata rana za su fuskanci mutuwa kuma a yi musu hisabi a gaban Mahalicci.
Kailani ya bayyana jimaminsa game da rasuwar tsohon shugaban ƙasan, wanda ya bayyana a matsayin shugaba mai gaskiya da jajircewa.
Yana mai cewa mutuwa tana da tabbataccen lokaci, kuma babu wanda zai rayu har abada a doron ƙasa.
“A gaskiya mun ji ba dadi, kamar yadda na faɗa a baya, mutuwa ba a iya kauce mata. Babu wanda zai zauna har abada a duniya, mutuwa dole ce kuma tana zuwa ne a lokacin da Ubangiji Ya ƙaddara."
"Abin da nake so na faɗa wa waɗannan shugabannin da ke aikawa da saƙonnin ta’aziyya, su sani cewa wata rana su ma za su mutu.
"Yadda suke tafiyar da wannan ƙasa da mummunan shugabanci, ya zama darasi a gare su, domin babu wanda ya san ranar mutuwarsa."
"Kada su ci gaba da wawure dukiyar ƙasa, suna sace abin da ya kamata a yi amfani da shi wajen amfanar da kowa."
- Farfesa Muhammad Kailani
Ya bayyana cewa gwamnatin Buhari ta faɗa hannun wasu shafaffu da mai, wanda hakan ya sa aka yi watsi da mutane nagari da suka tsaya tare da shugaban a baya.
An ba Shugaba Tinubu shawara
Ya shawarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya koyi darasi daga kurakuran da suka faru a lokacin Buhari.

Source: Facebook
"Sun karɓe gwamnati daga hannun Buhari, suka yi watsi da mutane nagari. Mutanenmu ba su ji daɗi ba. Ni kaina ban ji daɗi ba."
"Amma na yafe wa Buhari. Ba laifinsa ba ne. Ina fatan waɗanda ke kewaye da Tinubu ba za su bar abin da ya faru da Buhari ya maimaita kansa ba."
“Muna da shekaru biyu kafin wa’adin nan ya ƙare. Muna nan, muna goyon bayansa. Muna so a kawar da matsalar rashin tsaro gaba ɗaya a Najeriya."
"Halin ƙuncin rayuwa da muke ciki a yau, inda mutane ke cin abinci da wahala daga rana zuwa rana, bai kamata a Najeriya ba. Mu ne ƙasa mafi arziki a duniya, amma mutane na wahala kamar marasa gata."
- Farfesa Muhammad Kailani
Shekarau ya yi ta'aziyyar Buhari
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya yi ta'aziyyar rasuwar Muhammadu Buhari.
Shekarau ya nuna alhininsa kan rasuwar tsohon shugaban ƙasan na Najeriya wanda ya rasu a birnin Landan.
Tsohon gwamnan ya nuna cewa Najeriya ta yi rashin mutum wanda yake ƙaunarta tare da al'ummarta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


