Wata Sabuwa: Za a Yi wa Shugaba Buhari Addu'a a Coci Ranar Lahadi
- Shugaba Bola Tinubu ya amince da taron majalisar zartarwa na musamman domin girmama marigayi Muhammadu Buhari a Abuja
- Za a gudanar da taron ne bayan addu’ar uku a Daura, inda Mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima ya jagoranci tawagar gwamnati
- Za a ci gaba da bikin addu’o’i a ranar Juma’a da Lahadi a Babban Masallacin kasa da cocin kasa a Abuja domin neman gafara ga marigayin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirinta na gudanar da wani taron majalisar zartarwa ta musamman domin girmama tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari.
Wannan taro na musamman na cikin ayyukan girmamawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da su, domin karrama marigayi Buhari wanda ya shugabanci Najeriya.

Source: Twitter
Legit ta tattaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da ma'aikatar yada labarai da wayar da kan al'umma ta wallafa a X.
Za a gudanar da taron a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a yau Alhamis, da misalin karfe 5:00 na yamma, bayan kammala addu’ar kwanaki uku a garin Daura, Jihar Katsina.
Za a yi taron FEC don girmama Buhari
Taron majalisar zartarwa na musamman zai haɗa manyan jami’an gwamnati da suka haɗa da shugaban majalisar dattawa da na wakilai, da kuma bangaren shari’a na ƙasa.
Haka kuma za a gayyaci wakilan iyalan marigayin domin su halarci wannan muhimmin taro da ke nuni da girmamawa ga rayuwar jagoran da ya shugabanci Najeriya a matsayi daban-daban.
Za a yi hakan ne bayan Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jagoranci tawagar gwamnati a Daura wajen addu’ar uku ga Buhari.
Za a yi wa Buhari addu'a a masallaci da coci
A rahoton da tashar NTA ta wallafa a X, Legit ta gano cewa za a gudanar da addu’a ta musamman a Babban Masallacin Abuja a ranar Juma’a, 18 ga Yuli.
A nan ne za a haɗu da shugabannin addini da 'yan siyasa domin yi wa marigayin addu'ar rahama, kamar yadda aka saba.

Source: Facebook
A ranar Lahadi, 20 ga Yuli, za a gudanar da addu’ar musamman a wani coci da ke Abuja, domin bai wa mabiya addinin Kirista damar yin addu'a ga tsohon shugaban ƙasar.
Gwamnati na ci gaba da girmama Buhari
Tuni gwamnatin tarayya ta ɗauki wasu matakai na musamman domin karrama marigayin ciki har da bude rajistar ta'aziyya a ma'aikatu.
Wannan lamari na nuna matsayin da Muhammadu Buhari ke da shi a tarihin siyasar Najeriya, wanda ya ba da gudunmawa mai yawa a matsayinsa na soja da kuma shugaban farar hula.
An rufe majalisa saboda girmama Buhari
A wani rahoton, kun ji cewa majalisar kasa ta dakatar da aiki na tsawon kwana bakwai domin girmama marigayi Muhammadu Buhari.
Majalisar ta bayyana cewa an dauki matakin ne domin ba 'ya'yanta damar halartar jana'iza da ta'aziyyar tsohon shugaban kasar.
Baya ga dakatar da aiki, shugabannin majalisar dattawa da wakilai sun mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin a madadin 'yan kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

