Shettima, Atiku, Gwamnoni da Jiga Jigan da Suka Koma Gidan Buhari Awanni 24 bayan Birne Shi
- Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima tare da gwamna Dikko Radda sun halarci addu'ar uku a gidan Muhammadu Buhari
- An gudanar taron addu'ar ne domin rokon Allah gafarta wa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ranar Laraba a Daura
- Manyan jiga-jigan siyasa, ministoci na yanzu da tsofaffi sun halarci wannan addu'a ta bayan kwanaki uku da rasuwar Buhari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina - An gudanar da taron addu'ar uku domin rokon Allah Ya jikan tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a gidansa na Daura a jihar Katsina.
Taron ya haɗa manyan ’yan siyasa daga ɓangarori daban-daban, ciki har da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar.

Source: Twitter
Sanata Shettima ya tabbatar da hakan a wani saƙo mai haɗe da hotuna da ya wallafa a shafinsa na X jiya Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gudanar da addu'ar uku a gidan Buhari
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa da takwaransa na jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum sun halarci taron addu'ar a Daura.
Bayan kammala addu’o'i, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa rasuwar Buhari ta girgiza Shugaba Bola Ahmed Tinubu matuƙa.
Ya ce mutuwar Buhari babban rashi ne ba wai ga iyalinsa ko mutanen Daura ko na Jihar Katsina kaɗai ba, har ma da ƙasa baki ɗaya da nahiyar Afirka.
Shettima ya ƙara da cewa mutane daga sassa daban-daban na duniya sun kira domin jajanta wa Shugaba Tinubu bisa wannan babban rashi.
Ya yi addu’a ga Allah da ya jikansa da rahama, ya gafarta masa, ya sanya shi cikin Aljannatul Firdaus, tare da kare iyalansa da ya bari, kamar yadda Daily Trust ta kawo.
Jerin waɗanda suka koma gidan Buhari
Daga cikin manyan baki da suka halarci taron addu'ar akwai:
1. Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda
2. Gwamnan Borno, Fafesa Babagana Umaru Zulum
3. Ministar Harkokin Mata, Imaan Suleiman-Ibrahim
4. Ministan Noma da Samar da Abinci, Sanata Abubakar Kyari
5. Ministan Muhalli, Alhaji Balarabe Abbas
6. Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-tsare, Sanata Abubakar Bagudu
7. Ministan Shari’a kuma Antoni-Janar na Tarayya, Lateef Fagbemi (SAN)
8. Ƙaramar Ministar Babban Birnin Tarayya (FCT), Dr. Mariya Mahmoud
9. Ministan Ma’adanai da Bunkasa Karafa, Prince Shaibu Abubakar
10. Ƙaramin Ministan Ayyuka, Barr. Bello Goronyo
11. Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a 2023
12. Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Ambasada Babagana Kingibe
13. Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar
14. Tsohon Daraktan Hukumar Leken Asiri ta Ƙasa (NIA), Rufai Ahmed
15. Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika
16. Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai
17. Tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari
18. Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Farfesa Isah Ali Pantami

Kara karanta wannan
Yadda Atiku ya baro kasar waje, ya iso cikin dare domin jana'iza da makokin Buhari
19. Tsohon Ministan Abuja, Malam Musa Bello
20. Sarkin Daura, Mai Martaba Alhaji Umar Farouk
21. Tsohon Ministan Ruwa, Malam Suleiman Adamu da sauransu.
Buhari: Ministan Tinubu ya soki Atiku
A wani labarin, kun ji cewa Festus Keyamo (SAN) ya nuna takaicinsa kan yadda Atiku ya saki takardar barin PDP ana tsakiyar jimamin rasuwar Muhammadu Buhari.
Ministan sufurin jiragen sama ya ce bai kamata tsohon mataimakin shugaban ƙasa, ya fitar da wasikar ficewarsa daga PDP a daidai lokacin da Najeriya ke alhini ba.
Keyamo ya kalubalanci Atiku kan amfani da Tambarin Gwamnatin Tarayya, a cikin wasiƙarsa, yana mai cewa hakan ya sabawa doka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

