'Yana Tahiyar Sallah Ya Rasu': Shehi Ya Faɗi yadda Malami a Kano Ya Koma ga Allah

'Yana Tahiyar Sallah Ya Rasu': Shehi Ya Faɗi yadda Malami a Kano Ya Koma ga Allah

  • Sheikh Lawan Abubakar Triumph ya bayyana jimaminsa kan rasuwar Sheikh Abdullahi Yankaba, yana cewa Sunnah ta yi babban rashi a Kano
  • A cewarsa, Sheikh Yankaba ya sadaukar da rayuwarsa wajen yada ilimin Musulunci kuma rasuwarsa ta zo da alamomin mutanen kirki
  • Ya tuna yadda Ja’afar Adam da Malam Albani Zsriya suka rasu yayin ibada, yana mai cewa irin wannan mutuwa albishir ce ga Ahlus Sunnah

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Sheikh Lawan Abubakar Triumph ya yi ta'aziyyar babban malamin Musulunci da ya rasu a Kano.

Sheikh Triumph ya ce tabbas Sunnah ta yi rashin jajirtaccen malami wanda ya sadaukar da rayuwarsa kan hidimar addini.

Sheikh Triumph ya yi jimamin rasuwar Yankaba
Sheikh Triumph ya fadi yadda Malam Yankaba ya rasu a Kano. Hoto: Yasir Ramadan Gwale.
Source: Facebook

Sheikh Triumph ya yabawa gudunmawar Malam Yankaba

Hakan na cikin wani faifan bidiyo da Binyakub ya wallafa a Facebook a jiya Talata 15 ga watan Yulin 2025.

Kara karanta wannan

'Akwai alaƙa mai kyau tsakaninsu': Bidiyon haɗuwar Buhari da Tinubu na ƙarshe

A cikin bidiyon, malamin ya ce Sheikh Abdullahi Yankaba ya ba da gudunmawa sosai wurin habaka Musulunci.

Ya bayyana yadda ya samu labarin a halin da malamin ya rasu wanda ya ce abin alfahari ne ga Ahlus Sunnah.

Daga bisani ya yi wa Allah godiya da irin wadannan alamomi da Ubangiji ke nuna musu saboda dukan hanyar barinsu duniya ayoyi ne.

Ya ce:

"Na ji Farfesa Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo Allah ya kara masa lafiya ya ke fada iyalansa sun sanar da shi Malam Abdullahi Yankaba ya rasu yana sallar asuba.
"A tahiyar karshe ya rasu ba a ma san ya mutu ba, sai da aka ga zama ta yi tsawo sannan aka gane ya rasu.
"Muna yiwa Allah godiya da irin wadannan alamomi da albishir da Allah ya ke nunawa ga Ahlus Sunnah.
Triumph ya bayyana yadda Malam Yankaba ya rasu
Sheikh Lawan Triumph ya ce Malam Yankaba ya rasu yana sallah. Hoto: Sheikh Lawan Abubakar Triumph, Yasir Ramadan Gwale.
Source: Facebook

Sheikh ya tuna yadda aka kashe Malam Ja'afar

Sheikh Triumph ya tuno yadda aka yiwa Malam Ja'afar Mahmud Adam kisan gilla yayin da yake sallar asuba a jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan

'Masoyin Lagos ne: Tsohon gwamna ya faɗi alherin Buhari bayan rasuwarsa

Har ila yau, ya ce haka aka yi wa Malam Muhammad Adam watau Albaniy Zaria kisan gilla yayin da yake dawowa daga karatun hadisi.

Ya kara da cewa hakan ke nuna albishir ga Alhlus Sunnah da kuma aya kan yadda mabiyansu ke komawa ga mahaliccinsu ta hanyar hidima ga Musulunci.

A cewarsa:

"Kowa ya san mutuwar Malam Ja'afar shi ma yana sallar asuba a cikin sujjada aka harbe shi harbi na zalunci.
"Mutuwar Malam Albani ya dawo daga karatun hadisi yana kan hanyarsa ta komawa gida shi ma aka tare shi aka yi masa kisan gilla."

Babban malamin Musulunci ya rasu a Kano

A baya, mun ba ku labarin cewa fitaccen malamin addinin Musulunci a jihar Kano, Sheikh Dr Abdullahi Yankaba, ya rasu a safiyar ranar Litinin.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an gudanar da jana’izarsa da misalin ƙarfe 1:30 na rana a cibiyar Islahul Ummah da ke layin Umar Adamu, Yankaba a Kano.

Masu da’awa da almajirai sun bayyana alhini tare da addu’a ga Allah ya jikan marigayin, ya sanya shi a Aljannar Firdausi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.