ECOWAS: An Shawarci Tinubu bayan Kano Ta Soki Dokar Ɓatanci ga Annabi SAW
- Kungiyar MRA ta bukaci gwamnatin tarayya ta tuntubi gwamnatin Kano don aiwatar da hukuncin kotun ECOWAS kan dokokin batanci
- Kotun ECOWAS ta yanke cewa dokokin Kano na batanci sun sabawa yarjejeniyoyin kare hakkin dan Adam da Najeriya ta amince da su
- Kungiyar ta ce hukuncin dole ne, kuma gwamnati tana da nauyin doka da na ɗabi’a don tabbatar da bin ka’idojin kasa da kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Kungiyar kare hakkin ‘yan jarida wato Media Rights Agenda (MRA) ta ba gwamnatin tarayya shawara kan dokar kotun ECOWAS.
Kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta tattauna da jihar Kano kan hukuncin kotun ECOWAS game da dokar batanci

Source: Twitter
Kano: Hukuncin kotun ECOWAS kan batanci
A watan Afrilu, kotun ECOWAS ta yanke hukunci cewa dokokin batanci da ke Kano sun sabawa alkawuran kare hakkin dan Adam na kasa da kasa, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun ta bayyana cewa wadannan dokoki ba su dace da ‘yancin fadin albarkacin baki da dokokin yankin da na kasa da kasa ke tanada ba.
Har ila yau, kotun ta ce sashe na 382(b) a dokar laifuffukan shari’ar Musulunci ta Kano (2000) wanda ke ba da hukuncin kisa yana da tsanani.
Gwamnatin Kano ta mayar da martani tana cewa jihar na da damar kirkiro dokokin da ke da alaka da dabi’u da addinin al’ummarta.

Source: Facebook
Dokar batanci: An ba Tinubu shawara kan lamarin
A wata sanarwa ranar Laraba, Monday Arunsi na sashen shari’a na MRA ya ce gwamnatin tarayya na da hakkin doka da na ɗabi’a wajen tabbatar da dacewar doka.
Arunsi ya ce hukuncin kotun ECOWAS ya kara haskaka damuwar da ke akwai kan dokokin batanci a Kano da wasu jihohi a Najeriya.
Ya bukaci gwamnatin tarayya da ta nuna jagoranci ta hanyar tuntubar Kano da sauran jihohin da ke da irin wadannan dokoki, cewar rahoton ICIR.
Ya ce:
“Najeriya ba za ta rika zabin abin da za ta mutunta ba daga cikin alkawuranta na kasa da kasa.
“Hukuncin kotun ECOWAS yana da karfi na doka, kuma gwamnati na da nauyin tabbatar da daidaiton dokoki da yarjejeniyoyin kasa da kasa.”
Shawarar da aka ba majalisar dokoki, hukumomi
Sanarwar ta ce hukuncin kisa ya kamata ya tsaya kan manyan laifuffuka kamar kisan kai, ta’addanci ko kisan kare dangi, ba magana ko sabo ba.
Arunsi ya kuma bukaci majalisar dokoki ta kasa da hukumar kare hakkin dan Adam da sauran hukumomi su tabbatar da dacewar dokokin kasa.
Tinubu ya sauka daga shugabancin ECOWAS
Kun ji cewa shugaban Sierra Leone, Julius Bio, ya zama sabon shugaban ECOWAS bayan ya karɓi kujerar daga hannun Bola Tinubu a taron da aka yi a Abuja.
Bio ya ce zai maida hankali kan dawo da tsarin mulki, haɗin gwiwar tsaro da kuma bunƙasa tattalin arzikin yankin.
Sabon shugaban ya yabawa Tinubu saboda “kyakkyawan shugabanci” da jajircewa wajen dawo da zaman lafiya da farfaɗo da tattalin arzikin yankin ECOWAS.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

