'Ya Taɓa Korarmu kan N15': Diyar Buhari game da Tarbiyya da Mahaifinsu Ya ba Su

'Ya Taɓa Korarmu kan N15': Diyar Buhari game da Tarbiyya da Mahaifinsu Ya ba Su

  • Daya daga cikin ya'yan Muhammadu Buhari ta ce mahaifinsu ya koya musu kada su ci abin da ba nasu ba tun suna yara ƙanana
  • Hadiza Mohammed Buhari ta bayyana yadda suka ci N15 da aka rage musu bayan sayayya, amma Buhari ya kore su saboda rashin maida canji
  • Hadiza ta ce Buhari mutum ne mai sauƙin hali, marar son duniya, kuma suna fatan Allah ya saka masa da Aljanna

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Daura, Katsina - Ana cigaba da jimamin mutuwar tsohon shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari.

Daga cikin 'ya'yan tsohon shugaban ta bayyana irin tarbiyya da mahaifin nasu ya daura su a kai.

Diyar Buhari ta fadi tarbiyyar da suka samu
Diyar Buhari ta fadi abin da ke kewa daga mahaifinsu. Hoto: @BashirAhmaad.
Source: Twitter

Tarbiyyar da Buhari ya ba 'ya'yansa

Hadiza, da aka fi sani da Nana, ta faɗi haka ne yayin da take zantawa da manema labarai a gidan mahaifinta, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Diyar Buhari, Hadiza ta fadi tafarkin da mahaifinta ya dora yaransa a kai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadiza Mohammed Buhari ta ce mahaifinsu ya gina su da tarbiyya mai ƙarfi, musamman kada su ci hakkin wasu.

Ya ce:

“Ba zan manta ba shekaru da suka wuce muna yara, Baba ya tura mu siyo littattafan rubutu, bayan haka sai aka rage mana N15, madadin dawo da canjin wurin Baba, sai muka tsaya a wani shago muka sayi alewa da kuɗin.
“Da muka dawo gida, Baba ya tambaye mu inda canjin yake, muka ce mun kashe. Sai ya ce ya kamata mu dawo masa da kuɗin canji.
“Sannan ya ce mana, ‘Ya kamata ku dawo da canjin domin ni zan yanke hukunci ko zan bar ku da shi ko a’a.’
“Daga nan ya ce mana kada mu ci abin da ba namu ba, ko mu kwace hakkin wani. Muna godiya da tarbiyyar da muka samu.”
Tarbiyyar da Buhari ya ba yayansa kafin rasuwarsa
Diyar Buhari ta bayyana tarbiyya da mahaifinsu ya ɗaura su kai. Hoto: Muhammadu Buhari.
Source: Instagram

Diyar Buhari ta fadi kyawawan halayensa

Hadiza ta kuma bayyana rayuwar mahaifinta a matsayin mai sauƙi, mai tsoron Allah, kuma ba mai son tarin dukiya ba.

Kara karanta wannan

Farfesa Pantami ya tuna kyaututtuka 2 da Buhari ya yi masa da ba zai taɓa mantawa ba

“Rasuwar Baba ta girgiza mu. Duk mutuwa ba dadi gare ta. Amma muna godewa Allah da rayuwarsa mai sauƙi.
“Baba mutum ne marar buri. Kamar yadda kuke gani, babu wani abu mai ban mamaki a gidansa ko rayuwarsa.
“Muna godiya ga Allah bisa sauƙin halinsa, tawalarsa, gaskiyarsa da ladabinsa. Ina da tabbacin Baba yana wuri mafi alheri.
“Dukkanmu muna kan hanya ne, wasu sun isa jiya, wasu gobe. Allah ya ba mu ikon gamawa da kyau."

- Inji Hadiza

Diyar Buhari ta fadi halin da ta shiga

Kun ji cewa diyar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Noor ta bayyana baƙin cikin da ta shiga bayan rasuwar mahaifinta, a London da ke Burtaniya.

Tsohon shugaban ƙasa Buhari ya rasu a ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025, a asibiti da ke birnin London, yana da shekara 82, kuma an binne shi a gidansa na Daura.

Jama’a daga sassa daban-daban na Najeriya, ciki har da Bauchi, Jos da Gombe na ci gaba da gudanar da addu’o’in nema wa tsohon shugaban rahamar Allah Subhanahu wa Ta'ala.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.