Zambar N2.2bn: Babbar Kotu Ta Kawo Karshen Shari'ar Tsohon Gwamnan Ekiti da EFCC
- Tsohon gwamnan jihar Eikiti, Ayodele Fayose zai sarara bayan babbar kotun tarayya ta tabbatar masa da nasara a shari'arsa da hukumar EFCC
- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya ce dai ta gurfanar da tsohon gwamnan a kotu kan zargin tafka almundahanar kudi sama da N2.2bn
- Amma Fayose ya sha musanta zargin, inda ya bayyana cewa babu wani lokaci da ya yi amfani da damarsa ta gwamna wajen daka wa dukiyar jama'a wawa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Ekiti – Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta wanke tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, daga duk tuhume-tuhumen da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ke masa.
Kotun ta amince da ikirarin Fayose na cewa ba shi da laifi, inda ta yanke hukunci cewa EFCC ta kasa gabatar da hujjojin da za su sa a fara shari'a da shi kan zarge-zargen.

Source: Twitter
Jaridar The Nation ta wallafa cewa hukumar yaki da masu yiwa tattalin kasa ta'annati (EFCC) ce ta gurfanar da tsohon gwamnan a gaban kotu kan zargin wawashe dukiyar talakawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta yi hukunci kan tsohon gwamna
Vanguard News ta ruwaito cewa Mai Shari’a Chukwujekwu Aneke ne ya yanke wannan hukunci a safiyar ranar Talata.
Ya bayyana cewa bayan nazarin shari’ar, kotu ta gamsu cewa babu isassun hujjoji da suka danganta Ayodele Fayose da laifin da ake tuhumarsa da aikata wa.
A cewar kotun:
“Masu gabatar da kara sun kasa tabbatar da dangantakar wanda ake tuhuma da laifuffukan da ake zargi da har zai sa wannan kotu ta tilasta masa kare kansa."
EFCC ta tuhumi tsohon gwamnan Ekiti
Fayose ya shafe shekaru yana fuskantar shari’a dangane da zargin almundahana da almundahanar kuɗi da su ka haura N2.2bn, a lokacin da yake matsayin gwamnan jihar Ekiti.
EFCC ta zarge shi da karkatar da kuɗin gwamnati da kuma amfani da gurbatacciyar hanya wajen cire kuɗi daga baitul-mali.
Amma tsohon gwamna, Fayose ya sha musanta zargin, yana mai cewa bai taɓa wawurar dukiyar gwamnati domin bukatar kashin kai ba.

Source: Facebook
A ranar Talata dai kotun ta yi watsi da karar EFCC, ta na mai cewa babu hujja ko guda da ke gamsar da kotu cewa Fayose ya aikata laifin da ake tuhumarsa da shi.
Wannan hukunci na nufin an soke shari’ar gaba ɗaya, kuma tsohon gwamnan ya fita daga zargin da hukumar yaki da rashawa ta yi masa.
Tsohon gwamna ya goyi bayan Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya ce halin da Najeriya ke ciki yanzu a ƙarƙashin Bola Ahmed Tinubu ya fi na gwamnatin da ta gabata.
Fayose ya bayyana hakan ne yayin wata zantawa da manema labarai bayan ya kai wa shugaban ƙasa Tinubu ziyarar Barka da Sallah a Legas, tare da jaddada goyon bayansa ga shugaban.
Tsohon gwamnan, wanda jigo ne a PDP ya ƙara da cewa shugaba Tinubu na ɗaukar matakan da suka fi na Buhari tasiri wajen gyara matsalolin da suka dabaibaye rayuwar ‘yan Najeriya.
Asali: Legit.ng

