Atiku da El Rufa'i Sun Ziyarci Kabarin Buhari Kwana 1 da Birne Shi
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da Malam Nasir El-Rufai sun ziyarci kabarin Muhammadu Buhari domin yi masa addu'a
- Dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP, Peter Obi, ya isa Daura domin miƙa ta’aziyya ga iyalan tsohon shugaban ƙasar
- An shirya addu’ar uku a Daura, inda Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima zai jagoranci ministoci da masu alhinin rasuwar Buhari
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar tare da tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, sun ziyarci kabarin Muhammadu Buhari.
Haka zalika sun halarci addu’o’in da aka gudanar a gidan Buhari na Daura domin roƙon gafara ga tsohon shugaban ƙasar.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya isa Daura domin yin ta’aziyya ga iyalan marigayin.

Kara karanta wannan
Yadda Atiku ya baro kasar waje, ya iso cikin dare domin jana'iza da makokin Buhari
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan jana’izar Buhari da aka yi a ranar Talata, wacce ta kasance cike da alhini da alfarma ga wanda ya shugabanci Najeriya sau biyu a mulkin soja da kuma farar hula.
Peter Obi ya ziyarci gidan Buhari a Daura
An hango Peter Obi a gidan Buhari da ke Daura a safiyar Laraba, yana miƙa sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin.
Buhari dai ya rasu ne a birnin London a ranar Lahadi kuma aka yi masa jana’iza daidai da koyarwar Musulunci a garinsa na Daura a ranar Talata.
A cikin hotunan da Legit ta samu, bayan gaisawa da iyalan tsohon shugaban kasar, Peter Obi ya yi magana da sauran mutanen da suka je gaisuwa gidan.

Source: Facebook
Sojoji sun karrama Buhari da harbe-harbe
A wani salo na karramawa ta soja, manyan hafsoshin tsaro sun ɗauki akwatin gawar Buhari zuwa makabarta, an harba bindiga sau 21 a matsayin ban girma na ƙarshe.
Harbin bindigar ya ɗauki hankalin jama’a a Daura, inda aka nuna matuƙar mutuntawa ga rayuwa da gudummawar da Buhari ya bayar ga Najeriya.
Shettima zai jagoranci addu’ar 3 a Daura
A daya bangaren, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, tare da Gwamnan Borno, Babagana Zulum da Gwamnan Katsina, Dikko Umar Radda za su jagoranci addu'ar uku ga Buhari.
Tashar NTA ta wallafa a X cewa shugabannin da za su jagoranci addu'ar sun hada da wasu ministoci da masu alhinin rasuwar a Daura.
Rahotanni sun nuna cewa za su halarci addu’ar kwana uku wadda za a gudanar a gobe Alhamis a gidan Buhari da ke Daura.
Wannan na daga cikin umarnin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar domin nuna girmamawa ga marigayin.
Majalisa na jimamin rasuwar Buhari
A wani rahoton, kun ji cewa shugabannin majalisar dattawa da wakilai sun ayyana hutun mako guda kan rasuwar shugaba Buhari.
A bayanin da majalisar ta fitar, ta tabbatar da cewa ta dauki hutun ne domin ba mambobinta damar halartar jana'iza da ta'aziyya.
Haka zalika, a madadin 'yan Najeriya, majalisar ta mika sakon jaje ga iyalan shugaba Muhammadu Buhari da mutanen Katsina.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
