Dangote Ya Kinkimo Babban Aiki, Zai Gina Tashar Ruwa Mafi Girma a Najeriya

Dangote Ya Kinkimo Babban Aiki, Zai Gina Tashar Ruwa Mafi Girma a Najeriya

  • Shugaban rukunin kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana irin shirin da ya ke wajen kara inganta safarar gas daga Najeriya zuwa ketare
  • Aliko Dangote ya shigar da takardun izini domin gina tashar jiragen ruwa mafi girma da zurfi a Najeriya, a Olokola da ke jihar Ogun
  • Ya kara da bayyana cewa tuni shiri ya yi nisa, ganin yadda gwamnatin Dapo Abiodun ke marmarin aiki da yan kasuwa don habaka tattalin arziki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Ogun – Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya shigar da takardun izini domin fara aikin gina babbar tashar jiragen ruwa mafi zurfi a Najeriya, a jihar Ogun.

Dangote ya bayyana cewa yana kokarin fara aikin ne a sabon shirin tashar ruwa ta Atlantic da ake son ginawa a Olokola, jihar Ogun.

Kara karanta wannan

An fadi lokacin da ake sa ran birne Muhammadu Buhari a Daura

Alhaji Aliko Dangote
Dangote ya dauko babban aiki Hoto: Bloomberg
Source: Getty Images

A wata tattaunawa da Bloomberg, Dangote ya nuna cewa ya dawo da himma wajen gina manyan cibiyoyi saboda kyakkyawar mu’amalar Gwamna Dapo Abiodun da masu zuba jari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dangote ya dawo aiki gadan gadan

Daily Trust ta ruwaito cewa Dangote ya ce wannan tashar za ta taimaka wajen sauƙaƙa fitar da kaya daga Najeriya, daga ciki har da iskar gas, tare da ƙarfafa bunkasar masana'antun a fadin ƙasar.

A cewarsa:

"Ba wai muna son mu yi komai da kanmu ba ne, amma muna ganin idan muka fara hakan zai ƙarfafa gwiwar sauran 'yan kasuwa su shiga ciki."

Dangote ya bayyana cewa ya mika takardun neman izinin fara aikin tun watan da ya gabata, kuma yana fatan ci gaba da shirin cikin sauri.

Shirin Dangote kan tashar ruwa

A wata tattaunawa ta daban, Mataimakin Shugaban Kamfanin Dangote, Devakumar Edwin, ya bayyana cewa suna da shirin fitar da iskar gas daga jihar Legas zuwa kasuwannin duniya.

Kara karanta wannan

Tawagar shugaban kasa ta sauka a Katsina kan shirin birne Buhari

Shugaban kamfanin Dangote
Dangote zai gina tashar ruwa Hoto: Bloomberg
Source: Getty Images

Ya ce aikin zai haɗa da gina bututun gas daga yankin Neja Delta zuwa bakin teku, inda daga nan ne za a yi safararsa zuwa ketare.

A cewarsa:

“Muna so mu gudanar da babban aiki wanda zai kara yawan iskar da Najeriya ke fitarwa a yau.”
“Mun san inda gas ke da yawa, sai mu gina bututun da zai ratsa ta wuraren nan zuwa bakin teku.”

A ranar 26 ga Mayu, Dangote ya bayyana cewa kamfaninsa na sa ran samun kuɗi har Dala miliyan 7 a kowace rana daga sayar da takin zamani cikin shekaru biyu masu zuwa.

Dangote ya nuna shakku kan matatun Najeriya

A baya, mun wallafa cewa Shugaban rukunin kamfanin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana damuwa da rashin tabbaci game da yiwuwar gyaran matatun mai na gwamnatin tarayya.

Dangote ya ce dalilin da ya sa ya ke da shakku shi ne kasancewar matatun na amfani da tsofaffin kayan aiki da kuma rashin tsari mai kyau na tafiyar da su yadda ya kamata.

Dangote ya bayyana cewa kamfaninsa ya taɓa sayen wasu daga cikin matatun man a zamanin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, amma daga baya aka nemi ya mayar da su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng