Jerin Sunayen Sabbabin Jihohi 37 da Aka Buƙaci Ƙirƙirowa a Kano da Sauran Sassan Najeriya
- Majalisar Wakilai ta karɓi buƙatu 46 na kirƙiro sababbin jihohi a faɗin Najeriya yayin da take shirye-shiryen yi wa kundin tsarin mulki garambawul
- Majalisar ta karɓi waɗannan buƙatu ne ta hannun kwamitin da ta ɗora wa alhakin aikin gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999
- Daga cikin wadannan buƙatu da aka miƙa wa kwamitin, an nemi ƙirƙiro sababbin jihohi 37 a faɗin yankunan Najeriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Kwamitin Majalisar Wakilai ta Tarayya ya bayyana cewa zuwa yanzu, ya karɓi buƙatu 46 da suka nemi ƙirƙiro sababbin jihohi a faɗin Najeriya.
Kwamitin majalisar wanda aka ɗorawa alhakin gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, ya ce an kuma shigar da wasu buƙatu 117 na ƙirƙiro ƙarin ƙananan hukumomi.

Source: Facebook
Tribune Najeriya ta tattaro cewa wadannan ƙudurori da aka shigar daga kungiyoyi da dama sun shafi dukkanin shiyyoyin siyasa guda shida na ƙasar nan.
Jerin sunayen sababbin jihohi 37 da aka buƙata
Legit Hausa ta haɗa maku cikakken jerin sunayen jihohin da ake neman ƙirƙirowa kamar yadda kwamitin ya fitar:
Arewa maso Gabas
1. Jihar Savannah — daga Jihar Borno
2. Jihar Kwararafa — daga Jihar Taraba
3. Jihar Katagum— daga Jihar Bauchi
4. Jihar Amana — daga Jihar Adamawa
5. Jihar Sardauna — daga Jihar Taraba
6. Jihar Muri — daga Jihar Taraba
Arewa maso Yamma
7. Jihar Gurara — daga Jihar Kaduna
8. Sabuwar jihar Kaduna — daga Jihar Kaduna
9. Jihar Hadejia — daga Jihar Jigawa
10. Jihar Gobir — daga Jihar Sokoto
11. Jihar Kainji — daga jihohin Kebbi da Neja
12. Jihar Tiga — daga Jihar Kano
13. Jihar Ghari — daga Jihar Kano
Arewa ta Tsakiya
14. Edu State — daga Jihar Neja
15. Jihar Okun — daga Jihar Kogi
16. Jihar Okura — daga Jihar Kogi
17. Jihar Kudancin Filato — daga Jihar Filato
18. Jihar Lowland — daga Jihar Filato
19. Jihar Filato Sabon Yanki — daga Jihar Filato
20. Sabuwar jihar Kogi — daga jihohin Kogi, Nasarawa da Edo
21. Jihar Ifesowapo — daga Jihar Kwara
22. Jihar Abuja — daga babban birnin tarayya (FCT)
23. Jihar Apa — daga Jihar Benuwai
24. Jihar Apa-Agba — daga Jihar Benuwai
25. Jihar Ayatutu — daga Jihar Benuwai
Kudu maso Gabas
26. Jihar Orashi — daga Anambra, Imo da Ribas
27. Jihar Orlu — daga yankin Kudu Maso Gabas
28. Jihar Anioma — daga yankin Kudu Maso Gabas
29. Jihar Etiti — daga yankin Kudu Maso Gabas
30. Jihar Aba — daga yankin Kudu Maso Gabas
31. Jihar Adada — daga Jihar Enugu
Kudu maso Kudu
32. Jihar Atlantic City — daga Jihar Ribas
33. Jihar Bori — daga Jihar Ribas
34. Jihar Iwuroha — daga Jihar Ribas
35. Jihar Obolo — daga Jihar Akwa Ibom
36. Jihar Warri — daga Jihar Delta
37. Jihar Toru-Ebe — (babu cikakken bayani, yana yiwuwa daga Bayelsa)
An buƙaci raba Kano zuwa jihohi 2
A wani rahoton, kun ji cewa Kano ta buƙaci a raba ta zuwa jihohi biyu tare da kirkiro ƙarin ƙananan hukumomi 26 daga cikin 44 da ake da su a yanzu.
Hakan na cikin shawarwarin da gwamnatin Kano ta miƙa wa kwamitin gyaran kundin tsarin mulki a tarom jin ra'ayoyin jama'a da aka yi a Kaduna.
Ta ce hakan zai ƙara kusantar da gwamnati ga al'umma domin sauƙaƙa ci gaba da warware matsalolin da jama'a ke fuskanta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


