Farfesa Pantami Ya Tuna Kyaututtuka 2 da Buhari Ya Yi Masa da ba Zai Taɓa Mantawa ba

Farfesa Pantami Ya Tuna Kyaututtuka 2 da Buhari Ya Yi Masa da ba Zai Taɓa Mantawa ba

  • Farfesa Isa Ali Pantami ya ce ya zauna da Muhammadu Buhari na tsawon shekaru 24 kuma bai taba ganin rashin gaskiya a tare da shi ba
  • Pantami ya bayyana cewa Buhari mutum ne mai gaskiya, kishin kasa da jajircewa, yana tunawa da kyawawan halayensa da sadaukarwa ga jama'a
  • Ya ce maganar cewa Buhari bai kyauta ba gaskiya ba ne, ya sha samun kyauta daga gare shi har guda biyu da ba zai manta ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Daura, Katsina - Tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami ya yaba da halayen marigayi Muhammadu Buhari.

Farfesa Isa Pantami ya bayyana yadda ya san halin marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari tsawon shekaru 24.

Pantami ya fadi kyawawan halayen Buhari
Farfesa Pantami ya fadi kyaututtukan da Buhari ya ba shi. Hoto: Prof. Isa Ali Pantami.
Source: Facebook

Kyawawan halayen Buhari da Pantami ya zayyano

Hakan na cikin wani faifan bidiyo da Premier Radio ta wallafa a Facebook yayin hira da tsohon ministan.

Kara karanta wannan

Ana ci gaba da bayyana ayyukan alheran Buhari, Malami faɗI abin da ya sani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyon, Farfesa Pantami ya ce bai san Buhari da wani hali ba illa nagarta a iya zaman da suka yi da shi.

Ya bayyana Buhari a matsayin mutum mai gaskiya, kishin kasa da kuma ladabi, yana mai cewa kusancinsa da tsohon shugaban kasar ya tabbatar masa da wadannan halaye.

Ya ce:

“Muhammadu Buhari yana da gaskiya, za ka iya musanta hakan idan ba ka san shi ba ko kuma idan akwai cutar hassada, amma mu da muka zauna da shi shekaru da dama mun san hakan.”
“Na zauna da shi shekaru 24, kuma Allah ne shaida, ban taba kokwanto game da gaskiyarsa ba a duk zaman mu tare.”
Pantami ya fadi alherin da Buhari ya yi masa
Farfesa Pantami ya musanta cewa Buhari bai yin kyauta. Hoto: Muhammadu Buhari.
Source: Instagram

Kyaututtukan Buhari da Pantami ba zai manta ba

Farfesa Pantami ya kara da cewa tsohon shugaban kasa ya bar darasi ta fuskar tunani mai zurfi da sadaukar da kai ga sha’anin kasa.

Game da kyauta da aka ce Buhari bai cika yi ba, Farfesa Pantami ya tabbatar da cewa duka masu fadan ba su san shi ba ne.

Kara karanta wannan

Babbar jami'ar majalisar dinkin duniya ta yi wa Buhari shaida mai kyau

Ya ce shi ya sha samun manyan kyaututtuka daga Buhari inda ya ce idan ka ga bai yi ba ba shi da shi ne.

Ya kara da cewa:

"Wasu su kan ce wai Baba Buhari baya kyauta, Allah ya jikansa, wallahi yana kyauta, ni ina daga cikin wadanda na san ya min manyan kyauta guda biyu, idan ka ga bai yi ba ba shi da shi ne, shi bai ajiye abu.
"Zan iya ba da misalai na kyautar da ya min guda biyu ba wai iyakacinsu ba kenan amma manya ne da har abada ba zan iya manta su ba.
"Dukkansu da an kawo wani abu zai ce to ina Malam su ne masu jama'a a ba su a san yadda za a yi, akwai misalai da dama."

Hirar Pantami da Buhari kafin rasuwarsa

Mun ba ku labarin cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana yadda ya tsere wa aure ta hanyar shiga aikin soja.

Marigayin ya bayyana hakan ne a wata hira da Sheikh Isa Ali Pantami wanda ya taba zama minista a gwamnatinsa.

Buhari ya ce yana matashi ne wani baffansa ya zo Daura da nufin aurar da shi da ’yar sa, amma ya gudu ya shiga soja.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.