Yadda Atiku Ya Baro Kasar Waje, Ya Iso cikin Dare domin Jana'iza da Makokin Buhari

Yadda Atiku Ya Baro Kasar Waje, Ya Iso cikin Dare domin Jana'iza da Makokin Buhari

  • Bayanai sun bayyana a kan yadda labarin rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya riski Atiku Abubakar a kasar waje
  • Hadiminsa, AbdulRasheed Shehu ya bayyana cewa Atiku ya katse tafiyarsa daga ƙasar waje domin halartar jana’izar tsohon shugaban a Daura
  • Tsohon hadimin Buhari, Bashir Ahmad, ya nuna godiya ga Atiku bisa yadda ya nuna girma da mutuntawa ga marigayin shugaban ƙasa, Buhari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina – Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, na daga cikin fitattun ‘yan siyasar Najeriya da su ka halarci jana’izar marigayi Muhammadu Buhari, tsohon shugaban ƙasa.

An gudanar da jana’izar ne a wani fili da ke gefen gidan Buhari a Daura, jihar Katsina, sannan aka birne shi a wani sashe na gidansa jim kaɗan bayan sallar jana’iza.

Kara karanta wannan

"Babu wani ɓoye ɓoye," Bagos ya faɗi mutanen da suka ci amanar Shugaba Buhari

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da Atiki
Atiku ya halarci jana'izar Buhari Hoto: @MSIngawa
Source: Twitter

AbdulRasheed Shehu, hadimin Atiku, ya bayyana a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X cewa Atiku ya katse wata tafiya da ya ke yi a ƙasar waje domin ya samu damar halartar jana’izar Buhari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Atiku ya halarci jana'izar Buhari

Bashir Ahmad, ta sakon da ya wallafa a shafinsa na X ya tabbatar da yadda Atiku Abubakar ya katse tafiya domin gaggawar samun tarbar gawar tsohon shugaban kasa da yi mata sallah.

A cewar sakon farko da AbduRasheed ya wallafa a kan batun, ya ce:

“Ya katse tafiyar kasuwancinsa da ya fara a ranar Asabar, ya dawo Najeriya da safiyar Lahadi.
Ya tsaya a Daura domin halartar jana’izar, sannan ya halarci addu’o’in kwanaki uku na marigayi Baba. Waziri yana girmama Baba matuƙa. Allah ya gafarta masa. Ameen.”

Martanin tsohon hadimin Buhari ga Atiku

Tsohon hadimin shugaban ƙasa, Bashir Ahmad, ya bayyana jin daɗinsa da godiya ga Atiku Abubakar bisa yadda ya mutunta Buhari ta hanyar halartar jana’izarsa.

Kara karanta wannan

Shekarau ya yi alhinin rasuwar Buhari, ya bayyana wani halinsa da ya sani

Tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari
An birne Buhari a gidansa da ke Daura Hoto: Bashir Ahmad
Source: Facebook

Dubunnan yan kasar nan da suka hada da yan siyasa, malamai da talakawan gari ne suka halarci jana'izar marigayi Muhammadu Buhari bayan saukar gawarsa a Daura.

Ya ce:

“Waziri @atiku ya girmama Baba ƙwarai. Na samu labari cewa ba ma ya cikin ƙasar a lokacin, amma ya dawo cikin gaggawa.
Ya isa Daura tun da misalin 8.00 na safe. Ya kasance daga cikin shugabannin farko da suka je (jihar Katsina) domin yi wa Baba ban kwana na ƙarshe. Mun gode sosai, Alhaji.”

Malami ya fadi aikin Buhari

A baya, kun samu labarin cewa Tsohon Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya bayyana cewa marigayi Muhammadu Buhari ya jagoranci yaki da rashawa.

A cewar Malami, Buhari ya kafa tubalin da ya hana rashawa samun gurbin zama, inda ya ce an samu nasarori masu tarin yawa a manyan shari’o’in da suka shafi cin hanci da rashawa.

Ya ce gwamnatin Buhari ta kafa tsarin Asusun Bai ɗaya na Tarayya (TSA) da kuma Lambar Tantance Asusun Banki (BVN) domin hana karkatar da kuɗi da zurarewar kadarorin gwamnati.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng