Shekarau Ya Yi Alhinin Rasuwar Buhari, Ya Bayyana Wani Halinsa da Ya Sani
- Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya aika da saƙon ta'aziyyarsa kan rasuwar Muhammadu Buhari wanda ya mulki Najeriya
- Ibrahim Shekarau ya nuna alhininsa kan rasuwar tsohon shugaban ƙasan na Najeriya wanda ya rasu yana da shekara 82 a duniya a birnin Landan
- Shekarau ya nuna cewa Najeriya da al'ummarta za zu yi kewar ƙauna da kishin da Buhari yake da su kan ƙasar nan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya bayyana alhininsa kan rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Sanata Ibrahim Shekarau ya bayyana Buhari a matsayin jagora mai cikakkiyar ƙauna ga Najeriya da al’ummarta.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 14 ga watan Yulin 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Muhammadu Buhari ya bar duniya

Kara karanta wannan
Buhari: Diyar tsohon shugaban kasa ta fadi halin da ta shiga bayan rasuwar mahaifinta
Muhammadu Buhari dai ya rasu ne a ranar Lahadi, 13 ga watan Yulin 2025 a wani asibiti da ke birnin Landan.
Tsohon shugaban ƙasan ya yi bankwana da duniya ne sakamakon rashin lafiya wacce ba a bayyana ba.
A ranar Talata, 15 ga watan Yuli gawar tsohon shugaban ƙasan ta iso Najeriya ƙarƙashin rakiyar Kashim Shettima da wasu daga cikin iyalansa.
Shugaba Bola Tinubu da kansa ya karɓi gawar a filin jirgin sama na Umaru Musa da ke Katsina bayan isowarta Najeriya.
Daga nan an wuce da gawar zuwa mahaifarsa ta Daura inda aka yi masa sallar jana'iza tare da binne shi kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
Shekarau ya yi ta'aziyyar Buhari
A saƙon ta'aziyyarsa, Shekarau ya nuna baƙin cikinsa da kuma karɓar ƙaddarar Allah bayan samun labarin rasuwar.
Ya bayyana dangantakarsa da marigayin, wadda ta fara tun lokacin da ya fara siyasa a shekarar 2002.
“Tun daga shekarar 2002, lokacin da na shiga siyasa, kusancina da marigayi Shugaba Buhari ya bayyana mani yadda yake da ƙauna mai zurfi ga Najeriya da al’ummarta."
"A duk tattaunawata da shi, burin talaka da jin daɗin jama’a su ne ke gaban komai."
- Sanata Ibrahim Shekarau
Tsohon gwamnan ya jaddada cewa Najeriya da ƴan ƙasarta za su yi babban rashi sakamakon ƙwazon Buhari da ƙaunarsa ga ƙasa.

Source: Facebook
Ya kammala da yin addu'ar samun gafarar ubangiji ga marigayin wanda ya rasu yana da shekara 82 a duniya.
"Muna roƙon Allah Maɗaukaki Ya gafarta masa, Ya kuma sanya shi a Aljannatul Firdaus."
- Sanata Ibrahim Shekarau
An birne gawar Buhari a Daura
A wani labarin kuma, kun ji cewa an sada tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da makwancinsa na ƙarshe a ranar Talata, 15 ga watan Yulin 2025.
An birne gawar tsohon shugaban ƙasan ne a cikin gidansa da ke garin Daura bayan da aka yi masa sallar jana'iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
Jana'izar Buhari ta samu halartar mai girma Bola Tinubu tare da wasu manyan masu faɗa a ji a gwamnati a ciki da wajen Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
